Jiya Litinin 31 ga watan Yuli, maaikatar cinikayya, da babbar hukumar kwastam, da hukumar soja mai kula da kimiyya da fasaha da masanaantu, da sashen bunkasa kayan aikin soja na kwamitin koli na soja na PLA, sun ba da sanarwoyi guda biyu tare kan kayyade fitar da jiragen sama marasa matuka zuwa ketare.
Game da tambayar da aka yi kan mene ne ra’ayin kasar Sin na kaddamar da irin manufar, kakakin maaikatar kasuwancin kasar ya bayyana cewa, jiragen sama masu girman gaske kuma marasa matuka suna da wasu sifofi na soja, kuma kayyade fitar da su zuwa kasashen waje al’ada ce ta kasa da kasa.
Tun daga shekarar 2002, sannu a hankali kasar Sin ta aiwatar da matakan kayyade fitar da jiragen sama marasa matuka zuwa kasashen waje, kuma ikon sarrafawa da ka’idojin fasaha sun yi daidai da ka’idojin kasa da kasa.
A matsayinta na babbar kasar dake kera da kuma fitar da jiragen sama marasa matuka, kasar Sin ta yanke shawarar fadada kayyade fitar da jiragen sama marasa matuka yadda ya kamata bayan cikakken tantancewar da aka yi, ba domin wata kasa ko yanki ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)