A wannan makon ne majalisa ta fara tantance mutanen da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kake mata domin nada su mukaman ministoci.
Tun farko, shugaban kasa ya aika wa majalisa sunayen mutum 28 domin a tantance su, inda za su gurfana a gaban ‘yan majalisa domin amsa tambayoyi, sai dai kuma wasu daga ciki ‘yan majalisan ba su tsaurara tambayoyin ba, yayin da wasu kuma suka sha tambayoyi masu yawa. A yayin tantance ministocin, an samu takaddama a zauren majalisa har sai da aka bukaci wasu su kawo wa majalisa takardun haifuwa da shaidar takardun makarantarsu.
A ranar Alhamis da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta fitar da jerin sunayen wadanda Tinubu zai nada mukamin ministoci da zai kafa majalisar zartarwarsa, inda majalisa za ta tantance su kafin a tabbatar da nadin nasu.
Tinubu dai ya cika wa’adin watanni biyu da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi da dukkan gwamnonin su gabatar da jerin sunayen wadanda za su nada ga majalisar domin a tantance su a zauren majalisar.
Sunayen sun hada da tsoffin gwamnoni hudu, mata bakwai, ‘yan majalisa tsoffi da sababbi, an zabo su ne daga jihohi 25 cikin 36 na Nijeriya.
Tsarin mulkin kasar nan ya bai wa shugaban kasa damar zabo akalla minista daga kowace jiha, ana sa ran Tinubu zai mika wa majalisa karin sunayen mutane 11 a cikin kwanaki masu zuwa.
Tsofaffin gwamnonin guda hudu sun hada da Dabid Umahi, Nyesom Wike, Nasiru El-Rufai da kuma Abubakar Badaru.
Sauran sun hada da Abubakar Momoh, Ambassador Yusuf Miatama Tukur, Arch. Ahmed Dangiwa, Cif Uche Nnaji, Rt. Hon. Ekperipe Ekpo, Hon. Olubunmi Tunji Ojo, Mista Bello Muhammad G, Mista Dele Alake, Mista Lateef Fagbemi SAN, Mis-ta Muhammad Idris, Mista Olawale Edun, Mista Waheed Adebayo Adelabu, Farfe-sa Ali Pate, Professor Joseph Utseb, Sanata Abubakar Kyari, Sanata John Eno, da kuma Sanata Sani Abubakar Danladi.
A cikin wasikar da Tinubu ya aika wa majalisa, ya ce sunayen mutane 28 ne kashin farko na jerin sunayen ministocin da yake son nadawa, kuma ya yi alkawarin tura sauran nan da wani lokaci mai zuwa.
Sai dai wasu ‘yan Nijeriya sun bayyana shakku a kan yadda tsoffin ‘yan majalisa suke kubuta daga tambayoyin ‘yan majalisa.
‘Yan Nijeriya na sa ran ‘yan majalisun za su gudanar da aikin tantancewar ta han-yar da ta dace da abin da jama’a ke bukata.
An dai samu ce-ce-ku-ce a zauren majalisa a wurin tantance sunayen ministocin Shugaba Tinubu a lokacin da Farfesa Joseph Terlumun Utseb, wanda aka zaba daga Jihar Benuwai, ya ce ya fara karatun firamare tun yana dan shekara hudu.
Tun da farko yayin da yake gabatar da kansa, ya yi ikirarin an haife shi a 1980 kuma ya fara makarantar firamare a 1984.
Farfesa Utseb ya dage cewa an haife shi ne a shekarar 1980 kuma ya fara karatun firamare a shekarar 1984, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a zauren majalisar dattawa.
Duk da haka, bayan amsa tambayoyi kan abin da zai yi idan aka nada Ministan Al-barkatun Ruwa ta ya ya zai shawo kan ambaliyar ruwa a kasar, inda daga bisani aka bukaci Utseb ya tafi.
Shi ma Olubunmi Tunji-Ojo wanda shi dan majalisar wakilai ne ya bayyana cewa an haife shi a shekara ta 1982.
Ya dai kammala karatunsa ne a shekara ta 2005 daga jami’ar kasar Ingila, sannan ya yi bautar kasa a shekarar 2020 yana dan shekara 38 a lokacin da ya taba zama dan majalisar wakilai.
Yin bautar kasa ya kasance ne ga wadanda ke da shekaru kasa da 30.
Ojo ya bayyana cewa yana da shekaru 28 a lokacin da ya kammala karatunsa na jami’a, amma ya ci gaba da zama a kasar Ingila.
Ya yi nuni da cewa doka ta goyi bayan ya yi bautar kasa yana da shekaru 38 bayan ya dawo kasar nan.
Shi kuwa wanda aka zaba daga Jihar Taraba, Mohammed Danlandi ya sha am-bayoyi a lokacin tantancewa. An zarge shi da cewa kotun koli ta hana shi rike mukamin siyasa na tsawon shekaru 10.
Danlandi ya musanta wannan ikirarin, ya kara da cewa a halin yanzu lamarin yana gaban kotun koli.
Daga nan ne aka bukaci ya wuce a matsayinsa na tsohon dan majalisar dattawa.
Bayan haka, wanda aka zaba daga Jihar Sakkwato, Bello Mohammed, ya samu matsala a takardun karatunsa na kammala sakandare, inda a ciki aka samu darasi biyu kacal ya ji kuma ya samu gurbin shiga jami’a.
Wani dan majalisa ya so sanin yadda ya samu shiga jami’a ba tare da ya samu cin darashi biyar kamar yadda doka ta tanada.
Sai dai Bello ya ce abin da kundin tsarin mulki ya tanada shi ne, takardar shaidar kammala sakandare don tsayawa takara ba ta bukatar sai an ci darasi biyar ciki har da lissafi da turanci.
Ya ce ya yi wasu jarrabawar shaidar kammala makaranta da ya ba shi damar samun gurbin shiga jami’a. Sai dai bai bayar da sakamakon sauran jarrabawar da ya yi ga majalisar dattawa ba.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bukace shi da ya aika da wadannan takaddun zuwa zauren majalisar dattawa.
‘Yan majalisar sun gasa wa Betta Edu, Uju Ohaneye da Misis Imaan Sulaiman Ibra-him aya a hannu wajen tambayoyi har na kusan minti 30 kowanne su.