Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta karbi mulki Jihar Imo, a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Kwankwaso ya kasance tsohon gwamnan Jihar Kano ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar na kasa zai nuna himma sosai wajen ganin jam’iyyar ta kwace mulki a Imo, a matsayin daya daga cikin jihohin da ke da karfi a shiyyar ku-du maso gabas.
- Sin Ta Mikawa Gwamnatin Sudan Kashin Farko Na Tallafin Jin Kai
- Zanga-zangar Cire Tallafin Fetur: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Kungiyoyin Kwadago
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Jihar Imo, Mista Joshua Ele-kwachi jim kadan bayan ziyarar ban girma da dan takarar gwamna na jam’iyyar, Uche Ben Odunzeh da abokin takararsa Godstime Chukwubikem Samuel suka kai masa a Abuja.
Sai dai Kwankwaso ya bukaci Odunzeh da su ci gaba da jajircewa da mayar da hankali da kuma tabbatar da cewa bai yi watsi da alkawarin da ya yi wa al’ummarsa ba, musamman idan ya samu nasara, sannan kuma ya tabbatar ya hada kai da shugabannin jam’iyyar na kasa baki daya.
Kwankwaso ya kuma gargadi ‘ya’yan jam’iyyar na Imo da kuma dan takarar gwamnan da su yi aiki yadda ya kamata tare da shugabannin jam’iyyar don ganin NNPP ta samu nasara a Jihar Imo.
Tun da farko a nasa jawabin, dan takarar gwamna, Odunzeh, ya yi alkawarin nu-na jajircewa wajen ganin an hada kan masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar, musamman ganin yadda zabe ke gabatowa.
Ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar na kasa da su tabbatar da cewa kowa ya tashi tsaye don ganin jam’iyyar ta samu nasara a jihar.