Gwamnatin jihar Katsina ta amince da sayen hatsi da takin zamani domin rabawa marasa karfi da kuma manoman da ke fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Kwamishinan kudi na jihar, Hon. Bashir Tanimu Gambo ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar.
Bashir wanda ya sanar da hakan ga manema labarai da ke fadar gwamnatin jihar ya ce, hatsin da za a raba sun hada da Shinkafa, Masara da takin zamani.
Gwamnatin jihar ta yanke shawarar raba tallafin ne musamman ga marasa karfi domin rage musu radadin cire tallafin man fetur.
Kazalika, ya ce za a kafa kwamitin da zai sa Ido domin a tabbatar kayan sun isa ga wadanda aka tsara za su amfana da tallafin.