Arsenal ta samu wani kwarin guiwar lashe kofin Firimiya na bana yayinda ta doke kungiyar Pep Guardiola a bugun fenariti inda suka lashe Community Shield.
Bayan mintuna 70 na wasan,Cole Palmer ya ci wa Man City kwallo.
Sai dai Leandro Trossard ya rama kwallon a minti na 101 da fara tamaula.
Hakan dai ya dauki wasan zuwa bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Kevin de Bruyne ya buga kwallo amma ta daki turke.
Golan Arsenal ya hana kwallon Rodri shiga kafin Fabio Vieira ya jefa kwallon da tayi sanadiyar lashe kofinsu.
Arsenal ta jagoranci gasar ta Firimiya na tsawon kwanaki 248 a kakar wasan da ta wuce amma burinsu na daukar kofin ya ruguje.
Yayin da City ta dauki kofin kuma ta hada da sauran kofuna na gasar zakarun Turai da na FA.
Kocin Gunners Mikel Arteta ya fadi cewa a bayyane yake yana fatan samun nasara akan City, wacce ta doke kungiyarsa gida da waje a bara.
Manyan ‘yan wasan Arsenal da suka siyo Declan Rice da Kai Havertz da Jurrien Timber duk an basu damar buga wasansu na farko a Wembley.