Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Shige Da Fice ta Kasa (NIS), Wuraola Adepoju, ta tabbatar da goyon bayanta ga iyalan jami’an hukumar da ‘yan bindiga suka kai wa hari a kan iyakar Ilela da ke Jihar Sakkwato.
‘Yan bindigar sun kashe jami’an hukumar biyu tare da raunata wasu hudu.
- Manchester United Ta Cimma Yarjejeniya Da West Ham A Kan Maguire
- Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Zanga-zangar Da Suka Shirya
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ta bayyana cewa hukumar za ta kula da kudaden jinyar jami’an da suka samu rauni, kamar yadda wata sanarwa da kakakin hukumar, Dakta Dotun Aridegbe ya fitar.
Harin dai ya faru ne a wani shingen bincike da ke unguwar Gwadabawa a Jihar Sakkwato a karshen watan Yuli.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari shingen binciken da ke kauyen Mamman Suka a karamar hukumar Gwadabawa, inda suka kashe jami’ai biyu tare da raunata wasu hudu wanda daga bisani aka garzaya da su asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo, da ke Sakkwato.
Mukaddashiyar ta nuna alhininta game da lamarin, inda ta jinjina wa kwazon jami’an da suka yi artabu da maharan.
Har wa yau, ta kuma jajanta wa iyalan jami’an da suka rasu, inda ta tabbatar musu da cewa hidimar da suka yi wa kasa ba za ta tashi a banza ba.
Mukaddashiyar wadda a baya ta kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Sakkwato, ta bayyana shirin hukumar na gudanar da ayyuka ba tare da la’akari da kalubalen da suke fuskanta ba.
Ta kuma bai wa gwamnan tabbacin cewa NIS za ta ci gaba da kula da iyakokin kasar nan tare da samar da dabarun dakile kwararar bakin haure.
Ta samu rakiyar shugaban hukumar NIS na Jihar Sakkwato da kuma takwaransa na babban birnin tarayya, Kwanturola Tony Akuneme.