• Leadership Hausa
Thursday, November 30, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabar NIS Ta Ziyarci Jami’an Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Sakkwato

by Sadiq
4 months ago
in Labarai
0
Shugabar NIS Ta Ziyarci Jami’an Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Sakkwato
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Shige Da Fice ta Kasa (NIS), Wuraola Adepoju, ta tabbatar da goyon bayanta ga iyalan jami’an hukumar da ‘yan bindiga suka kai wa hari a kan iyakar Ilela da ke Jihar Sakkwato.

‘Yan bindigar sun kashe jami’an hukumar biyu tare da raunata wasu hudu.

  • Manchester United Ta Cimma Yarjejeniya Da West Ham A Kan Maguire
  • Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Zanga-zangar Da Suka Shirya

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ta bayyana cewa hukumar za ta kula da kudaden jinyar jami’an da suka samu rauni, kamar yadda wata sanarwa da kakakin hukumar, Dakta Dotun Aridegbe ya fitar.

Harin dai ya faru ne a wani shingen bincike da ke unguwar Gwadabawa a Jihar Sakkwato a karshen watan Yuli.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari shingen binciken da ke kauyen Mamman Suka a karamar hukumar Gwadabawa, inda suka kashe jami’ai biyu tare da raunata wasu hudu wanda daga bisani aka garzaya da su asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo, da ke Sakkwato.

Labarai Masu Nasaba

NNPP Ta Nemi EU, Amurka Da AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano

Sanatocin Arewacin Nijeriya Sun Matsa Wa Tinubu Lamba Kan Sake Bude Iyakar Nijar

NIS

Mukaddashiyar ta nuna alhininta game da lamarin, inda ta jinjina wa kwazon jami’an da suka yi artabu da maharan.

Har wa yau, ta kuma jajanta wa iyalan jami’an da suka rasu, inda ta tabbatar musu da cewa hidimar da suka yi wa kasa ba za ta tashi a banza ba.

Mukaddashiyar wadda a baya ta kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Sakkwato, ta bayyana shirin hukumar na gudanar da ayyuka ba tare da la’akari da kalubalen da suke fuskanta ba.

Ta kuma bai wa gwamnan tabbacin cewa NIS za ta ci gaba da kula da iyakokin kasar nan tare da samar da dabarun dakile kwararar bakin haure.

Ta samu rakiyar shugaban hukumar NIS na Jihar Sakkwato da kuma takwaransa na babban birnin tarayya, Kwanturola Tony Akuneme.

Tags: HariJami'aiNISSakkwatoYan bindigaZiyara
ShareTweetSendShare
Previous Post

Manchester United Ta Cimma Yarjejeniya Da West Ham A Kan Maguire

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Albanin Kuri A Gombe

Related

NNPP
Manyan Labarai

NNPP Ta Nemi EU, Amurka Da AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano

4 hours ago
Sanatocin Arewacin Nijeriya Sun Matsa Wa Tinubu Lamba Kan Sake Bude Iyakar Nijar
Labarai

Sanatocin Arewacin Nijeriya Sun Matsa Wa Tinubu Lamba Kan Sake Bude Iyakar Nijar

6 hours ago
Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Kujerar Gwamnan Adamawa
Labarai

Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Kujerar Gwamnan Adamawa

7 hours ago
Tinubu Ya Gabatar Da Kudurin Kasafin Kudin 2024 A Gaban Majalisa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Gabatar Da Kudurin Kasafin Kudin 2024 A Gaban Majalisa

14 hours ago
Za Mu Gudanar Da Bincike Kan Kundin Takardun Shari’ar Zaben Gwamnan Kano – NJC
Manyan Labarai

Za Mu Gudanar Da Bincike Kan Kundin Takardun Shari’ar Zaben Gwamnan Kano – NJC

15 hours ago
Al’ummar Jihohi 9 Na Arewacin Nijeriya Sun Gamsu Da Shirin ‘New Incentives For All’
Labarai

Al’ummar Jihohi 9 Na Arewacin Nijeriya Sun Gamsu Da Shirin ‘New Incentives For All’

16 hours ago
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Albanin Kuri A Gombe

'Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Albanin Kuri A Gombe

LABARAI MASU NASABA

NNPP

NNPP Ta Nemi EU, Amurka Da AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano

November 29, 2023
Ya Dace Kasashen Da Suka Ci Gaba Su Cika Alkawuran Da Suka Yi Game Da Sauyin Yanayi

Ministan Wajen Sin Ya Jaddada Shawarar Kafa Kasashe 2 A Matsayin Hanyar Warware Rikicin Falasdinu Da Isra’ila

November 29, 2023
Auto Draft

Ya Dace Kasashen Da Suka Ci Gaba Su Cika Alkawuran Da Suka Yi Game Da Sauyin Yanayi

November 29, 2023
Labarin Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin: Kimiyya Na Taimakawa Manoma Fita Daga Kangin Talauci

Labarin Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin: Kimiyya Na Taimakawa Manoma Fita Daga Kangin Talauci

November 29, 2023
OECD: Gdpn Sin Zai Karu Da Kashi 5.2 A 2023

OECD: Gdpn Sin Zai Karu Da Kashi 5.2 A 2023

November 29, 2023
Sanatocin Arewacin Nijeriya Sun Matsa Wa Tinubu Lamba Kan Sake Bude Iyakar Nijar

Sanatocin Arewacin Nijeriya Sun Matsa Wa Tinubu Lamba Kan Sake Bude Iyakar Nijar

November 29, 2023
Sin Na Ba Da Gudummawa Wajen Samar Da Abinci Da Tsarin Samar Da Kaya A Duniya

Sin Na Ba Da Gudummawa Wajen Samar Da Abinci Da Tsarin Samar Da Kaya A Duniya

November 29, 2023
An Kammala Aikin Bututun Karkashin Ruwa Na Sabuwar Hanyar Sin Da Ta Ratsa Teku

An Kammala Aikin Bututun Karkashin Ruwa Na Sabuwar Hanyar Sin Da Ta Ratsa Teku

November 29, 2023
Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Kujerar Gwamnan Adamawa

Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Kujerar Gwamnan Adamawa

November 29, 2023
Xi Ya Kai Rangadin Aiki A Birnin Shanghai

Xi Ya Kai Rangadin Aiki A Birnin Shanghai

November 29, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.