Guguwar juyin mulki da ta keta yankin Afirka ta Yamma tana bayar da mummunar alama watsi da tsarin dimokradiyya sannnu a hankali. A ra’ayinmu yadda ake neman a dawo da tsarin mulkin sojoji a tsakanin kasashe yankin Afiika ta Yanma abu ne mai tayar da hankali kuma bai kamata a amince da shi ba.
Yankin da ke fuskantar ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga yana kuma neman ya fuskanci juyin mulkin sojoji. Tuni aka hambarara da gwamnatin dimokradiyya ta kasashen Mali, Guinea da kuma Burkina Faso. Yanzu kuma sai ga shi a kasar Nijar.
- An Kammala Harhada Tushen Sashe Na SMR A Sin
- ECOWAS Ta Bada Umarnin Daukar Matakin Soji A Kan Gwamnatin Nijar
Wannan juyin mulkin da ya haska kasar Nijar a duniya ya faru ne a yayin da gungun sojoji a karkashin jagorancin dogarin shugaban kasa, Abdourahmane Tchiani, suka hambarar da zababben shugaban kasa Mohammed Basoum daga karagar mulki.
Nijar dai kasa ce mai fadin murabba’in kilomita 1,270,000 (Mil 490,000), wanda ya mayar da ita kasa mafi fadin kasa a yankin Afrika ta Yamma. Fiye da kashi 80 na kasar na mamaye ne da sararin sahara. Yawancin al’ummar kasar musulmai ne wadanda an kiyasta cewa sun kai mutum Miliyan 25. Kasar ta dade tana fama da kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar addinin musulunci guda 2 da suka hada da wanda ta taso daga kasar Mali a shekarar 2015, da dayar da ta shigo daga Arewa maso gabashin in Nijeriya. Saboda haka ne a lokacin da labari ya iso na cewa, an sake samun juyin mulki a kasar Nijar, juyin mulki na uku kenan a yankin a cikin shekara 3 dole hankalin al’ummar duniya ya tashi.
A martaninsu, kungiyoyin ECOWAS, UN, EU, AU da saura kasashen duniya sun yi watsi da karbar mulki ta hanyar juyin mulki sun kuma garkama wa Nijar takunkumi daban-daban. Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, a martanisa ya yi tir da juyin mulkin ya kuma yi watsi da duk wani kokarin kwace mulki ta hanyar da ba ta dimokradiyya ba musamman hanyoyin da za su yi barazana ga zaman lafiya da tsarin mulkin dimokradiyya a Nijar. Ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su kai zuciya nesa su kuma tabbatar da sun kare tsarin mulki gaba daya.
A taronsu karo na 55 da suka yi a Abuja, shugabannin kungiyar ECOWAS sun garkama wa kasar Nijar takunkumin da suka hada da kulle dukkan iyakokin kasar ta kasa da ta sama a tsakaninta da dukkan mambobin kungiyar, a wannan taron ne kuma suka zartar da ba gwamnatin sojojin masu juyin mulki wa’adin kwanaki bakwai na su dawo da Shugaban Kasa Muhammed Bazoum karagar mulki.
Kungiyar ta ECOWAS ta kuma dora wa Nijar takunkumin kwace kaddarorinta a bankunan da ke kasashe mambobin ECOWAS tare da haramta wa kasar zirga-zirga a tsakanbin kasashen kungiyar ECOWAS ta jiragen sama da kuma ta kasa.
Amma kuma sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi watsi da matsin lambar da ake yi musu, sun kuma ci gaba da garkuwa da Shugaba Basoum. Yayin da shugaban sojojin dan shekara 62, Tchiani, ya sanar da nada kansa a matsayin shugaban rikon kwarya na gwamnatin Nijar. Masu juyin mulkin sun ce sun yi hakan ne saboda yadda kasar ke neman tarwatsewa a sannu a hankali. Sun zargi shugaban kasar a kan rashin iya tafiyar da matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar da kuma yadda fatara da talauci suka addabi ‘yan kasa saboda tabarbarewa tattalin arzikin kasar.
A martaninsa game da juyin mulkin, Shugaba Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, ya ce, ba za a yarda da canjin gwamnati ta hanyar da bata dace ba, kuma ba za a yarda da hakan ba a dukkan kasashen Afrika, musamman ganin hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin ganin a daidaita al’amurra a yankin tare da dawo da tsarin dimokradiyya da mulki na gari.
Bayan karewar wa’adin da kungiyar ECOWAS ta ba jagororin juyin mulkin, sun yi gargadin cewa, duk wani mataki na soja da za a dauka a kan kokarin da suke yi na ceto kasarsu zai fuskanci martani mai kwari.
Mun yi takaicin yadda juyin mulki ke yaduwa a yankin Afrika ta yamma a daidai wannan lokacin da ake kokarin tabbatar da mulkin dimokradiyya a yankin, a kan haka muna masu shiga sahun al’ummar duniya na kira da a gaggauta dawo da mulkin dimokradiyya a Nijar da sauran kasashen da sojoji suka hambarar da zababbun shugabaninsu.
Muna kuma kira ga ECOWAS da sauran kungiyoyin duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da su yi taka-tsan-tsan wajen tafiyar da lamarin kasar Nijar don a kauce wa tashin hankali. Domin kuwa yekuwar yaki zai kara tagomashi da farin jinin sojojin kasar ne kawai wainda hakan zai kuma iya kaiwa ga tashin hankali a sassan kasar da ma wasu kasashe makota. Mun yi imanin cewa, tattauanwa da shugabanin masu juyin mulkin zai matukar taimakawa, ta yadda za su fito da tsari da jadawalin mayar da kasar tsarin mulkin dimokradiyya a nan gaba kadan.