A cikin shekara 44 da suka wuce shirin nan na samar da masa’anantu a yankin Arewa ya fuskanci turjiya da tabarbarewa sannu a hankali, inda daruruwar kamfanoni da gwamnati da bangaren masu zaman kansu suka kafa suka dukushe.
Binciken da LEADERSHIP Hausa ta yi a jihohi 17 cikin 19 na yankin arewacin Nijeriya ya tabbatar da cewa, shirin nan na samar da masa’annatu a a yankin arewa da marigayi Sadaunan Sakwatto, Sir Ahmadu Bello, ya yi wanda kuma ya samu goyon baya daga gwamnonin mulkin soja a karkashin shugabancin Janar Yakubu Gowon, basu samu kulawar da ya kamata a daga gwamnatocin da suka biyo bayansu.
- Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Haifar Da Da Mai Ido
- Fasahar Aikin Gona Da Ire-Iren Hatsi Masu Inganci Na Sin A Bikin Baje Kolin Uganda
Masu ruwa da tsaki a harkar masa’anantu da LEADERSHIP Hausa ta tattauna da su sun dora alhakin durkushewar kamfanoni a yankin arewa a kan shirin nan na sayar da hannun jari da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fito da shi sannan gwamnonin jihohi na lokacin suka runguna, shirin bai samu nasarar da ake bukata ba saboda sabbin wadanda suka sayi kamfanonin sun kasa zuba isassun jari da zai samar a ci gaba don wanzuwar da kamfanonin. An kuma zargi wadanda suka sayi kamfanonin da rashin iya gudanar da harkokin kamfanonin. A cewarsu lamarin ya ta’azara ne sakamakon matsalolin tsaro, rashin tsayayyun manufofin gwamnati da kuma rashin yanayi mai kyau da kamfanonin za su wanzu.
Jihohin da wannan lamarin ya shafa sun hada da Jihar Kwara mai kamfanoni 12, Nasarawa, 6, Borno, 8, Kaduna, 20, Filato, 7, Benuwai, 5, Bauchi, 6, Sakkwato,10, Neja, 5, Yobe, 2, da kuma jihar Adamawa mai kamfani 3.
Jihohn da basu da kididdga daga ma’aikatar ciniki da masa’anantu, da kungiya ‘yan kasuwa da zuba jari sun hada da Kano, Kebbi, Taraba, Jigawa, Gombe, Zamfara da kuma Jihar Katsina.
A jihar Katsina, jami’in da wakilinmu ya tattauna da shi cewa ya yi, kashi 90 na kamfanonin jihar sun durkushe, yayin ta takwararsa na jhar Kebbi ya ce, ana da akalla kamfanoni 30 a jihar amma a halin yanzu kadan ne daga cikin su ke aiki, ya ce, kamfanoni 3 ne kawai ke aiki cikin kamfanoni masu sarrafa shinkafa da rogo.
Haka kuma LEADERSHIP Hausa ta gano cewa, a Jihar Kwara, kamfanonin da suka durkushe a jihar tun kafin dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999 sun hada da ‘Kwara Tedtiles’, ‘Kwara Match Company (MATCO)’, ‘Tate and Lyle Sugar Company’, ‘Kwara Papers Conberter’, dukkan su mallakin gwamnatin Jihar Kwara.
Kamfanoni masu zaman kansu da suka durkushe a jihar Kwara sun hada da ‘Global Soap Detergent’,Ilorin, ‘Coca Cola Bottling Plant, Ilorin’, ‘Double Cola Company, Ilorin’, ‘Okin Biscuits, Offa’ da kuma ‘Ijagbo Breweries’.
Kamfanonin gwmanatin tarayya kamar su ‘Nigeria Sugar Company, Bacita’, ‘Nigerian Paper Mill, Jebba’, da kuma ‘Nigerian Yeast and Alcoholic Manufacturing Company (NIYAMCO)’ sun dukushe ne sakamakon tsarin sayar da hannun jari na gwamnatin Obasanjo.
A Jihar Nasarawa kuwa, ‘yan kalilan din kamfanoni mallakin gwamnatin tarayya da jihar sun durkushe sakamakon rashin yanayi mai kyau da zai ciyar da kasuwanci gaba.
Cikin kamfanonin da suka wanzu a jhar suka kuma durkushe daga baya sun hada da ‘Delta Prospectors Limited ‘ da Ultramodern Processing Plant wadanda suke a kan hanyar Jos a cikin garin Lafia a babba birnin jihar.
Kamfanin da aka kafa a shekarar 1995 tana harka ne a bangaren ma’adanin da ake kira ‘Barites’ inda suke aikawa ga kamfanoni masu sarrafa albarkatun man fetur da iskar gas.
Kamfanin ya samu ci gabnr da ya kamata sai abubuwa suka lalace sakamakon tsare-tsaren gwmnatin farar hula na Obasanjo. Amma a halin yanzu an yi shekaru kamfanonin sun durkushe.
Cikin kamfanoni masu zaman kansu da suka durkushe a Jihar Nasarawa akwai ‘Oil Chem Nigeria Limited’ wanda yake a hanyar Makurdi a garin Lafia, babban birnin Jihar.
An kafa kamfanin ne a shekarar 2001, yana kuma bayar da harkokin tallafi ne ga kamfanonin albarkatin man fetur da iskar gas na ciki da kasashen wajen kasar nan, bayan shekara 7 da fara aiki a hakin yanzu kamfanin ya durkushe babu wani labari.
Bayan durkushewar kamfanoni masu zaman kansu, wasu kamfanonin gwamnatocin jihohi da suka samu bunkasa a lokacin da aka kaddamar da su, sun shiga matsala da ta kai ga an cefanar da su ga wasu kamfanoni masu zaman kansu.
Wadannan kamfanonin sun kuma hada da kamfanin taki na ‘Fertiliser Blending Plants’, wanda ke a garuruwan Lafia da Keffi, da ‘Nasarawa Beef Factory’ da ke Masaka a karamar hukumar Karu, ‘Nasarawa Sacks Factory’ ta Akwanga, wanda aka kafa a shekarar 2002 da kuma kamfanin ruwa na ‘Nas Spring Water Company Ltd’ da ke garin Lafia, wanda aka kafa a shekarar 2001.
Wakilanmu sun gano cewa, dukkan kamfanonin da durkushewar ta shafa sai da aka cefanar da su kafin suka ci gaba da harkokinsu.
Shugaban cibiyar masana’antu da harkokin kasuwanci na Jihar Borno, Alhaji Ahmed Ashemi, ya bayyana cewa, an yi asarar guraben aiki fiye da 10,000 a fadin jihar sakamakon durkushear masana’antu da kuma harkokin ‘yan ta’adda a sassan jihar.
Ya kuma kara da cewa, kamfanonin da za su iya bayar da aiki ga mutun daga 20 zuwa 30 duk sun durkushe, sai dai matsaikaitan masana’natu kamar gidajen biredi, tailelo da masu yin ruwan kwalba dana leda suke tafi da harkokinsu.
Shugaban na BOCCIMA ya kuma ce, kafin bayyanar kungiyar Boko Haram yawancin kamfanonin da ke Jihgar Borno da ake samu a babban birnin Jihar Maiduguri kamar kamfanin fulawa da ke unguwar Umarari cikin garin Maiduguri yana dan aiki sama sama.
Haka shi ma shugaban kungiyar masu masa’anantu na jihar Katsina, Abba Yusuf, ya bayyana cewa, masana’antu da kananan kamfanoni a jihar da saurar sassan kasar nan duk sun kamo hanyar durkushewa gaba daya.
Ya koka a kan cewa, matsalolin tattalin arziki da matsalartsaro sune a kang aba wajen durkusar da kamfanoni sannu a hankali a sassan Nijeriya.
Ya bayar da misali da Mekera Hotel, wadda ke da ma’aikata 36 amma bayan shekaru tana harkokin kasuwancinta a halin yanzu saboda matsalar tsaro sai aka wayi gari babu wani bako da yake kwana a otal din, kuma gashi suna fuskantar kalubaken sayen man dizel a kan Naira 800 kowanne lita a kullum.
Ya bukaci gwamnati ta gaggauuta kawo dauki ta hanyar bayar da tallafi ga amsu masana’antu don su samu fita daga cikin matsalolin tattalin arziki dana tsaro da ake fuskanta a kasar nan.
A jihar Kaduna ma labarin iri daya ne, don bayani ya nuna cewa, kamfanoni fiye da 20 duk sun durkushe saboda rashin isashen wutar lantarki, rashin tsayyen tsare-tsaren gwamnati da kuma mastalar tsaro da ake fama da shi a kasar nan.
 A tattaunawarsa da wakilinmu, shugaban kungiyar masu masana’anantu na jihar, Usman Saulawa, ya ce, shigowar kayayyaki daga kasashen waje cikin kasar nan na daga cikin manya-manyan abuuwan da suka haifar da durkushewar kamfanoni a Nijeriya.
Ya kuma yaba wa gwamnatain tsohon gwmanan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a kokarin da ya yi na jawo masu zuba jari na cikin gida da kasashen waje duk kuwa da matsalar tsaro da ke fuskanta a jihar.
Saulawa ya kuma kara da cewa, wasu kamfanonin da suka durkushe a cikin shekara 20 da suka wuce sun hada da ‘Starled Manufacturers, ‘Kaduna machine tools, ‘Kaduna Ware’ da ‘Zaria Industries,’ ‘Kaduna aluminum’ da kuma ‘Kaduna tedtile industries
A jihar Filato kuwa, kamfanin da yake ci gaba da aiki duk da cewa ya yi sanyi sosai shi ne kamfanin ‘NASCO Group of Companbies’ wanda yake a hanyar zuwa filin jirgin sama na jihar.
An kafa kamfanin ne a garin Jos a shekarar 1963, yana a kan gaba a daukar ma’aikata a fadin arewacin kasar nan gaba daya.
Sai kuma kamfanin ‘Jos International Breweries (JIB) Plc’ wanda suke yin barasan nan masu suna ‘Rock’ da ‘Class Lager beer’. Kamfanin kuma na yin abin shan nan mai suna ‘Royal Malt’ wanda al’umma yankin arewa ta tsakiya da bangaren jihar Kaduna ke amfani da su.
A shekarar 1975 Gwamna Joseph Gomwalk ya kafa kamfanin, kamfanin na da karfin daukar ma’aikata da suka kai 4,000, amma duk kokarin da gwamnatocin da suka biyo daga baya na farfado da kamfanin ya ci tira.
Haka kuma kamfanin mulmula karafuna na ‘Jos Steel Rolling Mill’ da gwamnatin Alhaji Shehu Shagari ya kafa a sheklarar 1980 yana nan a durkushe.
A shekarun baya, kamfanin sarrafa fatu na ‘Naraguta Leather Works’ da ke kauyen Naraguta kusa da garin Jos ya shahara amma a yau ya zama tarihi.
Tsohon shugaban cibiyar masana’antu na jihar Filato, Da Bulus Dareng, ya bayyana wa wakilimu cewa, jama’a basa wani maganar ci gaban masa’anantu a halin yanzu saboda babu tsaro a koina a fadin jihar.
Haka kuma babban sakataren kungiyar masu masana’antu na kasa mai kula da yankin arewa ta tsakiya da arewa ta gabas, Egwilo Augustine, ya ce, babban matsalar da ake fuskanta shi ne na tsaro da tsadar kayyakin aiki wanda hakan na faruwa ne saboda janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi.
A Jihar Benuwai manyan kamfanonin da ke tafiyar da tattalin arzikin jihar a shekarun baya wadanda suka hada da ‘Otukpo Burnt Bricks Company’, ‘Taraku Mills Company’, ‘Benue Cement (Dangote Cement)’ da ‘Benue Plastic Industry (Ben-King)’ wanda tuni aka cefanar da su. A halin yanzu bayan kamfani siminti na ‘Dangote Cement’ duk sauran kamfanonin sun durkushe gaba daya.
A nasa ba’asin shugaban kungiyar masu masana’antu na Jihar Bauchi, Sani Tahir ya bayana cewa, kamfanoni da dama sun durkushe a jihar ne saboda rashin bin ka’dojin kula da tafiyar da kamfanoni.
Tahir ya sanarwa wakilinmu cewa, bincike ya nuna cewa, rashin samar da cikakken kididdga na yadda ake tafiyar da kamfani yana haifar da rushewar harkokiin kasuwanci musamman in aka kasa tantance tsakanin riba da jari, haka kuma rashin kwarewar gudanar da harkar kasuwanci sun taimaka matuka wajen durkushewar kamfanoni a jihar Bauchi.
Shugaban ya kuma ce, wani dalilin kuma shi ne na kafa kamfani a a bayan gari inda babu wuta da da ruwan famfo, wanda hakan ya kan zama matsala da kamfanin har ta durkushe, saboda ba za a iya gudaar da kamfani ta hanyar janareta ba saboda tsadar man fetur da gas.
Wakilimu ya gano cewa, domin farfado da kamfanonin, a shekarar data wuce ne gwamnatin jihar ta cefanar da kamfanoni 6, kamfanoin da aka cefanar sun hada a ‘Bauchi Meat Factory’, ‘Bauchi Furniture Company’, ‘Wikki Hotels and Tours’, ‘Zaranda Hotel’, ‘Bauchi State Fertiliser Blending Company’ da kuma ‘Galambi Cattle Ranch’.
A jihar Kebbi kuma LEADERSHIP Hausa ta gano cewa, a lokacin da aka kirkiro da jihar a ranar 17 ga watan Agusta na shekarar, 1991 kamfani 3 a ake da su a jihar, sun kuma hada da ‘Plastic Industry’ da ke Bulasa ta karamar hukumar Birnin Kebbi mallakin wani dan kasuwa mai suna Alhaji Na’amo Abubakar Birnin Kebbi, kuma tsohon shugaban Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Waziri Umaru, da kamfanin sarrafa Rogo na garin Kalgo dake karamar hukumar Kalgo, mallakin Alhaji Noma Kalgo.
A tsakanin shekarar 2003 da 2015, an samu nasarar kafa wasu kamfanoni kamar haka ‘Labana Rice Mills’ da ke cikin garin Birnin Kebbi, ’Lolo Rice Mills Company’ a Kamba da ke karamar hukumar Dandi da kuma kamfanin shinkafa na ‘Bakaba Rice Mills’ a garin Argungu.
Babban sakataren ma’aikatar masana’antu na jihar, Abubakar Kigo Dakingari, ya bayyana cewa, a kwai kamfanoni masu aik da wadanda suka durkushe fiye da 30 a jihar.
Ya ce, wadanda suke aiki sun hada da kamfanonin shinkafa da na sarrafa rogo da kamfanonin roba, wasu kamfanoninsun mutu ne saboda tsadar wutar lamtarki da kuma yadda wasu ma’aikata suka yi allubazaranci da kudaden kamfanin.
Haka labarin yake a Jihar Adamawa inda kamfanonin gwmanati irinsu ‘Mubi Burnt Bricks Industry’, ‘Gombi Chalk Company’, da kamfanin taki na ‘Fertiliser Blending Company’ duk sun durkishe sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da kuma matsallolin tsaro a fadin jihar.
A jihar Sakkwato kuwa, manyan kamfanonin da suka bayar da gaggrumin gudummawa wajen bunkasa jihar duk sun durkushe, kuma babu wani kokari na sake farfado da su da ake yi a nan kusa.
Kamfanonin da suka bayar da gudummawar bunkasa rayuwar al’umma jihar a shekarun baya wandanda a yanzu duk sun durkushe sun hada dana mallakin gwmanati dana masu zaman kansu, ciki har da ‘Labella Ceramics’, ‘Haske Rice Mill’, ‘Sokoto Leather Industry’, ‘Wurno Plastic Limited’, ‘Sokoto Furniture Company’ da kuma ‘Wurno Construction Materials’ sauran sun kuma hada da ’Zaki Bottling Company’, ‘Sokoto Beberages Limited’, ‘Sokoto Food Industry’, ‘Sokoto Match Industry’, ‘Bafarawa Flour Mill’, ‘Sokoto Foam Limited’, ‘Sokoto Dairies Limited’ da kuma ‘Shamrock Fertilizer Company’.
A Jihar Neja kuma wadanda wakilanmu suka tatauana dasu sun bayyana cewa, harkokin ‘yan ta’adda ya matukar durkusar da harkokin kamfanoi a fadin jihar.
Kamfanonin da suka durkushe a jihar sun hada da ‘WAMCO (Peak Milk)’, ‘Chi Limited (Chibita)’, ‘NEON’, ‘Irish Diary’, da kuma ‘Hail Consortium’ sauran sun kuma hada da ‘Crystal Talc’ da ‘Kalgara’ dukkan su a garin Kagara.
Haka ma a Jihar Gombe yawancin kamfanonin da aka kafa don sarrafa kayan gona duk sun durkushe, cikin su kuma akwai ‘Manto Processing Company’ a garin Kumo, a karamar humumar Akko wanda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar don sarrafa manwgaro da tumatir.
Jihar Yobe da Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da suke a baya wajen mallakar kamfanoni, a kan haka duka kamfanonin da aka kafa don samarwa da al’umma jihar ayyukan yi duk sun mutu, sauran da suka rage a halin yanzu sun hada da ‘Lee Group of Company producing shoes’, ‘Mats, Room Carpets and other plastic goods’, Majestic Dairy, ‘Danmodi Rice Mills’, ‘Jigawa Rice Mills’ da ‘CGC Marbles Company’ duk suna aiki a halin yanzu.
Jihar Taraba ma bata da kamfanoni masu yawa kuma tana daga cikin jihohi da basu da manyan kamfanoni wanda hakan ne ma ya sa basu da kungiyar masana’antu da cinikayya a jihar.
Duk da shirin samar da dokokin yin harkar kasuwanci a cikin sauki har yanzu masu kamfanoni na ci gaba da kokawa a kan yadda ake tastsar haraji daga gare su a jihar Kogi wanda hakan yake taimakawa wajen durkushewar harkokin kasuwanci a fadin jihar.
Wani masanin tattallin arziki mai suna Farfesa AbdulGafar Ijaya, daga Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara ya bayana cewa, samar da kayan aiki, wutar lantarki za su iya taimakawa wajen farfado da kamfanonin da suka durkushe a fadin yanki arewacin Nijeriya da Nijeriya baki daya.
Ya kuma karfafa bukatar gwamnati ta yi maganin matsalolin tsaro wanda hakan yake hana al’umma a yankunan karkara aikin gona wanda kuma daga nan ne ake samar da kayan da ake sarrafawa a kamfanonin.
Shi ma wani masani a bangaren tattalin arziki, Dauda Danliman, ya bukaci a zuba jari mai yawa don samar da hanyoyi da kayan aiki a yankunan da kamfanonin suke, wanda ta haka za a tabbatar da wanzuwar kamfanoni a sassan arewacin Nijeriya dama Nijeriya baki daya.
Ya kuma nema a kawo karshen yadda ake shigo da kayayyaki daga ketare tare da bayar da tallafi ga masu masana’antu don su samu saukin gudanar da harkokinsu cikin kasa.