Wasu barayi hudu sun kutsa gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ibrahim Halliru Musa da aka fi sani da Albani Kuri cikin daren ranar Laraba inda suka yi masa kisan gilla.
Barayin sun kutsa gidan malamin ne dake Bobona a Anguwar Tabra ta Karamar Hukumar Akko rufe da fuskokinsu, inda suka bukaci ya basu kudi.
- An Gudanr Da Taron Dadadden Kwamitin Kula Da Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afrika Ta Kudu
- Birnin Jinhua Na Kara Kyautata Alaka Da Kasashen Afirka
Kakakin rundunar ‘yansanda a Jihar ASP Mahid Muazu Abubakar, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, yana mai cewa kawo lokacin hada wannan rahoto ba su kama kowa ba kan lamarin, amma bincike na ci gaba da gudana kamar yadda kwamishinan ‘yansandan jihar CP Okua Etim ya ba da umarni.
Mahid Mu’azu ya ce marigayin ya yi kokarin gane daya daga cikin barayin ne ta hanyar yaye fuskarsa dake rufe, lamarin da ya sa suka sassare shi da adda a wuya da kai da kuma baya, har ma da caccaka masa wuka a kirji.
Ficewarsu ke da wuya aka dauke shi zuwa asibiti, amma saboda munanan raunukan da suka yi masa ba a jima da isa asibitin ba ya rasu.
Shugaban kungiyar Izala a jihar Sheikh Salisu Muhammad Gombe ya yi Allah wadai tare da bayyana takaici kan kisan, yana mai bayyana rashin Sheikh Albani Kuri a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi baki daya.
Yace suna fatan binciken da jami’an tsaro ke yi zai haifar da da mai ido ta hanyar kamowa da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aika-aika.
Marigayi malamin addinin Musuluncin ya rasu yana da shekaru 46, ya bar mata biyu da ‘ya’ya hudu da mahaifiyarsa da kuma ‘yan uwa da dama.
Tuni dai aka yi jana’izar Marigayi Sheikh Albani Kuri a masallacin Izala da ke Bolari, wadda ya samu halartar dubban jama’a daga nesa da kusa ciki har da gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya.
A baya bayan nan dai ana samun karuwar shiga gidaje da kwacen waya da sauran miyagun laifuka a jihar, lamarin da masharhanta ke danganta shi da rashin ayyukan yi da zaman banza tsakanin matasa.
Suna ganin kara tsaurara tsaro da samarwa matasa abun yi ka iya taimakawa matuka wajen rage matsalar.