Kasar Australia mai masaukin baki ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta mata ta 2023 a karon farko bayan da ta doke Faransa a bugun fenareti a filin wasa na Brisbane.
Bayan mintuna 120 babu ci,Australia ta yi nasara da ci 7-6 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
- Kane Ya Kammala Komawa Bayern Munich Bayan Shekaru 20 A Spurs
- Da Dumi-Dumi: Bayern Munchen Ta Kulla Yarjejeniya Da Tottenham Domin Siyan Kane
Mai tsaron gidan Australiya, Mackenzie Arnold, ta hana kwallo shiga har sau hudu a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Talla
Sai dai masu masaukin baki ne suka samu nasara kaiwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta mata.
Australia za ta kara da Ingila ko Colombia a filin wasa na Australia da ke Sydney a ranar 16 ga Agusta da karfe 11 na rana.
Talla