Gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele ya bayyana a gaban kotu a yau Alhamis domin amsa zargi kan tuhume-tuhume 20 da ake masa da suka shafi rashawa.
Lauyoyin gwamnati ne suka shigar da sabbin zarge-zarge a kansa da suke da nasaba da ‘amfani da ofishinsa wajen bayar da kwangila ba bisa ka’ida ba’.
- Sojojin Nijar Na Neman Goyon Bayan Kasashe Daban-Daban
- Kotu Ta Dakatar Da Sanata Ali Ndume Kan Yi Wa Wani Malami A Abuja Karan Tsaye
Ana zargin Emefiele da hada baki da wata ma’aikaciyar CBN da kuma wani kamfani wajen siyo motoci masu sulke 98 ba tare da sun bi ka’idojin bayar da kwangila ba.
Rahotanni sun ce matar da ake zarginsu tare darakta ce a CBN kuma kawo yanzu ba su mayar da martani ba kan wadannan zarge-zargen.
A watan Yuni ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele kuma hukumomi suka gabatar da shi gaban kuliya a Jihar Legas bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.