Akalla mutum 1,087,875 ne suka rasa matsugunansu sakamakon yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da masu satar shanu da kuma masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a jihohin arewa maso yammacin Nijeriya.
Rikicin ya fi shafar mata da yara, kashi 54 mata da kashi 56 na yara sun yi gudun hijira a Jihar Katsina, kuma jimillar mutanen da lamarin ya shafa sun kai 223,473.
An bayyana hakan ne a taron kaddamar da shirin sasanta rikici da sulhu a yankin arewa maso yammacin Nijeriya a hukumance, wanda hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta shirya a Babban Birnin Jihar Katsina a ranar Litinin.
Shugaban hukumar ta IOM, Laurent De Boeck, ya bayyana cewa arewa maso yamma na fama da rikice-rikice tun daga shekarar 2014, wanda ya kai ga gudanar da bincike a watan Oktoban 2022 don gano karuwar tashe-tashen hankula, wanda ya shafi kimanin mutum sama da miliyan daya, a cikin wannan adadi kashi 29 cikin 100 ‘yan asalin Jihar Katsina ne.
Ya kuma kara tabbatar da cewa IOM, cibiyar habaka dimokuradiyya tare da taimakon Kungiyar Tarayyar Turai sun hada kai da gwamnatin Jihar Katsina domin inganta tsarin shiri sulhunta al’umma a jihar, da nufin rage rikice-rikice da inganta shirin samar da zaman lafiya a cikin gida da rage radadin talauci da inganta albarkatun kasa na arewa maso yammacin Nijeriya.
Aikin wanda ya kai kimanin watanni 18, ya fara ne tun daga Janairu 2022 zuwa Yuli 2023, za a gudanar da shi a kananan hukumomi hudu da suka hada da Dandume, Danmusa, Batsari da Jibia a Jihar Katsina.
Shima da yake jawabi a madadin gwamnatin jihar, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Nasiru Muazu Danmusa, ya gode wa abokan hulda na kasa da kasa kan wannan gagarimin aikin. Ya ce jihar na bukatar karin tallafi domin yaki da rashin tsaro da ya addabi wasu sassan jihar.