Bayan kammalar taron kolin BRICS na kwanakin baya, masharhanta na ta tofa albarkacin bakinsu, game da tasirin kyakkyawan yanayin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, musamman ta la’akari da kalaman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya furta, yayin taron tattaunawa a tsakanin shugabannin Sin da na Afirka a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
A cikin kalaman shugaba Xi, ya bayyana bukatar dake akwai ta Sin da Afirka su yi hadin gwiwa, wajen sa kaimi ga tabbatar da odar kasa da kasa bisa adalci, da kiyaye yanayin duniya mai zaman lafiya da tsaro, da kuma raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga kowa.
Ko shakka babu, akasarin masu sharhi sun gamsu da manufar kasar Sin, ta “A Gudu Tare A Tsira Tare”, inda suke kafa misali da yadda hadin gwiwar sassan biyu ya samar da wani ginshiki, na gina muhimman ababen more rayuwa masu ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar nahiyar Afirka, matakin dake taimakawa matuka ga bunkasa masana’antu, da kyautata hada-hadar cinikayya a kasashen Afirka.
A zahiri take cewa, a baya bayan nan, kasar Sin ta wuce gaba a fannin yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, inda ba ya ga batun tattalin arziki da cinikayya, Sin din na daukar kasashen nahiyar Afirka a matsayin abokan gina makoma, wadda ’yan baya za su ci gajiyarta.
Wasu daga masharhanta ma na ganin yayin da alakar Sin da Afirka ke kara zurfafa, nan gaba sassan biyu za su karkata ga kulla hadin gwiwar raya fannin manyan fasahohi, irinsu kwaikwayon tunanin bil adama, da binciken sararin samaniya, da sauran muhimman sassa da duniya ke mayar da hankali yanzu a kansu.
Fatan da dukkanin sassan nahiyar Afirka ke yi a halin yanzu, shi ne dorewar kyakkyawar dangantaka mai armashi tsakaninsu da kasar Sin, ta yadda za su ci gaba da cin gajiya, da bunkasa kawancen gargajiya mai dadadden tarihi tsakaninsu da Sin. (Saminu Alhassan)