Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar ya bukaci malamai da su rika shawartar masu mulki kan shugabanci nagari.
Sarkin Musulmin ya yi wannan kiran ne a Abuja wajen taron bitar ga malaman addini kan harkokin kiwon lafiya a matakin farko.
- Ranar Litinin Za A Kaddamar Da Jirgin Kasan Legas Da Zai Rika Jigilar Fasinja 175,000
- NIS Ta Bude Ofishin Samar Da Ingantaccen Fasfo A Zariya
Kamfanin dillancin labara na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA) ne suka shirya taron.
Sarkin Musulmi ya ce yana da kyau malamai su kasance masu gaskiya da rikon amana a yayin da suke da kusanci da shugabannin siyasa.
“Shugabannin addini sukan rike mukamai masu gwabi kuma suna iya kawo sauyi ga rayuwar al’umma.
“Ta hanyar ba da shawara ta gaskiya ne za a iya samun ingantacciyar shugabanci da zai ba da gudummawa ga rayuwar al’ummarsu gaba daya.
“Kyakkyawan sadarwa tsakanin malamai da shugabannin siyasa na iya haifar da fahimtar juna, hadin kai da kuma cimma manufofin da aka saka a gaba.
“A duk lokacin da malamai ke fada wa masu mulki gaskiya, zai taimaka wajen yanke hukunci da manufofi wadanda suka dogara a kan ingantattun bayanai da suka dace da dabi’u da ka’idodi,” in ji shi.
Shi ma shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) Archbishop Daniel Okoh, ya bukaci karin hadin kai da hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa domin inganta harkokin kiwon lafiya musamman a yankunan karkara.
 Okoh, wanda ya bayyana muhimmiyar rawar da malaman addini suke takawa wajen bayar da shawarwari da wayar da kan jama’a, ya ce dole ne a hada kai da shugabannin siyasa domin inganta harkar kiwon lafiyar kasar nan.
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya yaba wa gudunmawar da malamai ke bayarwa wajen samar da kiwon lafiya a kasar nan.
Ministan ya jaddada mahimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da malaman addini.
Pate ya ja hankali kan yadda fannin kiwon lafiya ke ci gaba da bunkasa, ya ce akwai bukatar yin hadin gwiwa a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya da malamai.
“Ta hanyar hadin kai ne za a samu damar ilimantar da juna da kuma sanar da jama’a game da abubuwan da ke faruwa, za mu tabbatar da cewa an samar da ayyuka masu inganci na kiwon lafiya ga ‘yan Nijeriya,” in ji shi.
Babban daraktan hukumar NPHCDA, Dakta Faisal Shuaib, ya yi kira ga malamai da su ba da himma gudunmuwa wajen inganta harkokin kiwon lafiya a matakin farko da kyautata jin dadin al’umma.
“Manufar wannan taro na musamman shi ne, rigakafin cutar kansa ta mahaifa ta hanyar allurer HPB,” in ji shi.
Ya bukaci shugabannin addini da su bayar da shawarwarin rigakafi a cibiyoyinsu.
Shugaban NPHCDA ya jaddada karfin hadin kai da aiki tare wajen inganta lafiya da walwalan al’umma.
Ya ce ta hanyar hada kai ne malamai da ma’aikatan kiwon lafiya za su bayar da gudummuwa ga harkokin lafiya da kuma ci gaban kasa.
NAN ta ruwaito cewa taron ya samu halartar malaman addini, ma’aikatan lafiya da masu ruwa da tsaki kan harkokin lafiya da manyan jami’an gudanarwa na ma’aikatar lafiya da NPHCDA.
Taron dai an yi shi ne domin kara inganta fahimtar malamai game da allurar rigakafi da sauran shirye-shiryen kiwon lafiya tare da wayar da kan al’umma kan amfanin rigakafin.