A irin zamantakewa ta yanzu ba duka iyali ne suke gaisuwa tsakanin miji da mata ba, gara ma dai tsakanin ‘ya’ya da iyayensu ko yayye da kannai.
Wannan ba yana nuna yin gaisuwa tsakanin ma’aurata ba shi da kyau ba ne, tarbiyya ce mai kyau, amma matasan yanzu na ganin kwana daki daya ko gado daya ya dauke wannan bukatar gaisuwar, musamman saboda ganin ana tare kowanne lokaci.
- Neymar Ya Zarce Pele A Matsayin Wanda Yafi Zurawa Kasar Brazil Kwallaye
- Tinubu Ya Amince Da Gina Gidaje 1,000 A Jihohin Arewa 7 – Shettima
Wannan na faruwa ne a irin yanayin da zamani ya kawo na canji a halin zamantakewa da ake fuskanta, a kowanne bangaren rayuwa. Dole ne a daidai wannan gaba a rika samun akasi, saboda sauyin da yake shigowa.
Hajiya Aishatu Gidado Idris wata fitacciyar marubuciya kuma mai ba da shawarwari kan zamantakewar iyali ta rubuta cewa, dole ne a kokarin daidaita jiya da yau a zamantakewar rayuwa sai an fuskanci turjiya da kalubale daga al’umma. Wannan haka yake ko a tarihin duniya, duk lokacin da wani sabon tunani ya zo ya ci karo da tsohon tsari, sakamakon ba ya kyau, a wani lokaci ma har asarar rai ake yi da dukiya, saboda nuna bore daga jama’a. Kamar yadda yanzu abubuwan da suka biyo bayan wannan shiri ya daga hankalin masu gabatar da shirin, iyalinsu, mutuncinsu da mu’amalarsu da jama’a, sakamakon yadda aka kasa fahimtar su da mummunar fassarar da ake musu.
A cikin lafazi mai nuna dacin rai, “Hajiya Halima Ben Omar ta ce, shirin Mata A Yau bai taba kawo wata fatawa ko shawara da ta soki koyarwar addinin Musulunci ba, amma muna kokarin ganin an samu canji ga wasu abubuwa da al’ada ce ta kawo su ba addini ba. Sai dai abin mamaki wasu da ko kallon shirin ba su taba yi ba, sun bi duniya suna yada cewa ana fada da koyarwar addini.”
Lallai ne ya kamata wannan ya zama darasi gare mu duka, musamman tashar Arewa 24 da masu shirin Mata A Yau, su sani ana hallare da su, kuma kurar su ta riga da ta yi kuka tuntuni, don haka abu kadan ne za su yi ya zama matsala. Ya kamata su kara hattara da taka-tsantsan, kuma su rika tauna kalamansu suna sanya hikima cikin fadakarwar da suke yi.
Sannan a kokarinsu na ganin sun kawo sauyi da cigaban rayuwar mata su rika fahimtar yanayin al’ummar da suke ciki, tsaurinta kan sha’anin addini da al’ada, da yadda canji ke wuyar samuwa a rayuwar Malam Bahaushe. Haka kuma su rika tuntubar malamai a kai-a kai ana samun fahimtar juna da karin haske kan wasu batutuwan da suke so su bijiro da shi. Na san shirin yana cike da kwararru, dan boko da malamai. Lallai a kara sa ido sosai!
Ya zama wajibi shugabannin tashar Arewa 24 su tashi tsaye wajen ganin sun yi wa kansu gyaran fuska, sun hada kai da malamai da masu fada a ji don kyautata yadda jama’a ke yi musu kallon jakadun yahudawa, masu yaki da addini da gurbata tarbiyya. Su kuma samar da wasu shirye-shirye da jama’a za su gamsu da su cewa, mummunan zaton da ake yi musu ba gaskiya ba ne.
Gare mu masu kallo, yana da kyau mu fahimci cewa kowacce tashar talabijin ko rediyo akwai manufar kafata, kamar yadda na bayyana a farko. Ba zai yiwu kowacce tasha ta zama kamar Sunnah TB ko NTA ba. Akasari tashoshin talabijin na zamani sun fi mayar da hankali ne kan fadakarwa da nishadantarwa. Shi ya sa ko a Arewa 24 bangaren nishadi ke da muhimmanci, domin da shi ne ake daukar hankalin matasa ta yadda manufofin tashar na yaki da tsattsauran ra’ayin addini, cin zarafin mata, da shugabanci nagari, za su samu shiga zukatan matasa.