Shugaban Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya ce bai taba yin kira ga Kiristoci da su sayi bindigogi don kare kansu ba.
Faston, ya fadi hakan ne a ranar Lahadi a wani shirin talabijin na kai tsaye na godiya na wata-wata na cocin.
- Mummunar Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 18 A Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan
- Masani: Amurka Take Yada Karairayin Aikin Tilas Don Bata Sunan Kasar Sin
“Ban taba cewa Kiristoci su je su sayi bindigogi ba. Samson, a cikin Littafi Mai-Tsarki bai yi fada da bindigogi ba, ”
Bayanin ya zo ne a kan rahotannin kafofin watsa labarai cewa Faston ya ce yanzu “wuta-da-wuta” ce ga duk wani hari da aka kai wa Kiristoci.
“Kada ku sayi bindigogi. Ku dama kisa ba halinku ba ne. Dole ne mu tabbatar cewa shaidanu ba su zo cocinmu ba, don haka kar ku je ku sayi bindigogi,’’ inji shi.
A ranar 2 ga watan Yuli ne dai Fasto Adeboye, ya bukaci mabiya cocin da kada su ji tsoron halartar cocin saboda harin da ‘yan ta’adda suka kai a coci a garin Owo na jihar Ondo.
A baya-bayan nan ne wasu mahara suka kai hari wata coci a garin Owo a Jihar Ondo, inda suka kashe mutane masu tarin yawa da suke tsaka da yin ibada.