Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Kano ta tabbatar da bullar cutar amai da gudawa a birnin Kano.
Babban jami’in kula da cututtuka masu yaduwa na ma’aikatar, Sulaiman Iliyasu ne, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano.
- 2023: PDP Na Bukatar Hadi Kai Don Kayar Da APC – Makarfi
- Badakalar Kudin Makamai: PDP Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Buratai
Ya ce an samu rahoton bullar cutar a karamar hukumar Danbatta wadda har aka samu asarar rayukan mutane biyu.
“A watan Afrilu mun samu rahoton bullar cutar amai da gudawa a Danbatta wadda daga nan kuma sai cutar ta bulla a karamar hukumar Gwarzo”.
Dakta Iliyasu ya ce “Ya zuwa yanzu sama da mutane 25 zuwa 30 ne suka kamu da cutar a kwaryar birnin Kano kamar yadda sakamakon gwajin da muka yi ya tabbatar”.
A cewarsa yanzu haka kananan hukumomin da suka samu ɓullar cutar sun haɗa da karamar hukumar Dala, Ungoggo, karamar hukumar Birni da kuma Tarauni.
Sai dai ya bukaci al’umma da su kara kula da tsaftar muhallansu da kuma kai rahoton duk wata cuta da ta bulla ga hukumomin lafiya don daukar matakin gaggawa.
Ita dai cutar amai da gudawa wadda ake kira Kwalara, na bulla ne a sanadin rashin tsaftace muhalli kama daga kan abinci da ake ci zuwa gyaran jiki da sauransu.
Idan mutum ya kamu ya kan dinga yin amai ko gudawa, a wasu lokutan ma duka biyun har ta kai ga mutum ya galabaita idan ba a ba shi kulawa a kan lokaci ba.