Dakta Jamila Bio Ibrahim, ‘yar asalin jihar Kwara kuma ‘ya ce ga Ibrahim Bio, tsohon ministan wasanni a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Jamila, ‘yar shekara 37 ce da haihuwa a duniya kuma kwararriyar Likita ce ‘yar Siyasa.
Kazalika, Bio ta kasance mai kira ga tabbatar da bin shirye-shiryen ci gaban zaman takewar rayuwa (SDGs) da ke karkashin ofishin majalisar dinkin duniya.
Gwagwarmayarta a Siyasa:
Kafin a nada ta a mukamin shugabar Mata matasa ta kasa (PYWF) na jami’iyyar APC, ta kasance tana rike da mukamin Mataimakiya ta musamman ga gwamnan jihar Kwara a fannin kiwon lafiya.
Sauran gudunmawar da ta bayar:
Jamila, ta yi ayyukan jin kai daban-daban, mussamman a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya a karkashin shirin kwamitin fadar shugaban kasa.
Kazalika, ta kasance mai hakilon son ganin ci gaban Mata Matasa, mussamman don a dama da su a harkar Siyasa kuma su bayar da ta su gudunmawar wajen gina kasa.
Karrama wa Da Lambobin Yabo Da Ta Samu:
- An karramata da Lambar yabo ta jakadar tsafta a Nijeriya
- Kungiyar wanzar da zaman lafiya ta duniya ta ba ta lambar yabo ta jakadiyar wanzar da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya.
- An karrama ta da babbar lambar yabo kan gudunmwar da ta bayar a fannin ilimin boko da SDGs da ke karkashin kulawar UNESCO a Nijeriya.
- Ta taba wakiltar Nijeriya da kuma jihar Kwara, matsayin kakaki a taron kungiyoyin kasashen duniya kamar irinsu majalisar dinkin duniya (AU) da kuma kungiyar hadin kan Afirka (AU).