Babbar kotun majistari a jihar Kaduna ta yankewa wata mai sayar da kaya ‘yar shekara 28 mai suna, Vivian Bernard, hukuncin zaman gidan gyaran hali na watanni 12 kan satar katin wayar wanda take yi wa aiki da kimar kudin katin ya kai Naira 275,400.
Vivian wadda take da zama a yankin Karshi da ke jihar, an gurfanar da ita ne a gaban kotun kan zargin cin amana da kuma sata.
- Tsohon Mataimakin Sakataren NUJ Zai Kai INEC Kotu Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna
- Sauyin Kudi: Gwamnati Ta Bukaci Kotu Ta Kori Karar Da Kaduna, Kogi Da Zamfara Suka Shigar
Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Emmanuel, ya yankewa Vivian hukuncin ne ba tare da biyan wata tara ba, bayan ta amasa tuhumar da ake yi mata.
Da yake yanke hukuncin, Alkalin Kotun, Emmanuel ya ce, ya yanke hukuncin ne ganin yadda wadda ake tuhuma ta amasa laifinta.
Alkalin ya kuma umarci Vivian da ta biya David Williams wanda ya maka ta a gaban kotun Naira 275, 400 ko kuma kotun ta kara mata wani wa’adin zama a gidan gyaran halin har na watanni takwas.
Tun a farko, dan sanda mai gabatar da karar, Insfekta Chidi Leo, ya sheda wa kotun cewa, Vivian ta aikata laifin ne a ranar 27 na watan Agusta a anguwar Sabon Tasha da ke jihar, da misalin karfe 3.00 na rana.
Leo ya ci gaba da cewa, mai karar David Williams, ya dauki Vivian aiki ne a matsayin mai sayar masa da kaya kusan watanni biyar da suka gabata.
A cewar Leo, laifin sata ya sabawa sashe na 243 da sashe na 271 na dokar final kod ta jihar Kaduna ta shekarar 2017.