Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar APC a zaben 2023, Ambasada Air Marshall Sadique Baba Abubakar, ya sha alwashin daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke na karar da ya shigar.
Idan za a tuna dai a ranar Laraba 20 ga watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi ta kori karar da APC da dan takararta Sadique Abubakar suka shigar da ke kalubalantar nasarar da Gwamna Bala Muhammad na PDP ya samu a matsayin gwamnan jihar.
Kotun ta kori karar ce bisa dalilin cewa korafin da APC take yi bai da inganci tare da tabbatar da Bala Muhammad a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Bauchi.
Sai dai a martaninsa, dan takarar APC Sadique Baba Abubakar ya ki amincewa da hukuncin tare da cewa za su yi dukkanin abun da ya dace domin kwato hakkinsu a kotun daukaka kara.
A wani sako faifayin bidiyo da ya tura wa magoya bayansa, Sadique Abubakar ya ce, za su cigaba da gwagwarmaya har sai sun ga abun da ya ture wa buzu nadi.
“Mun yanke hukuncin za mu daukaka kara za mu tafi kotu na gaba, kuma bayan wannan kotun, ko’ina za mu je za mu je sai mun kai kololuwa wajen tabbatar da cewa an kwato wa al’umma hakkinsu, a karshen al’amari Allah ne yake yi.”
“Na bai wa lauyoyina umarni lallai su daukaka kara mu ci gaba kuma muna takama da Allah.
“Muna da tabbacin Allah zai kwato mana wannan kujerar ya dawo mana da ita da izininsa. A matsayinmu na shugabanni za mu yi dukkanin abun da ya dace domin ganin ba mu ja da baya ba a wannan gwagwarmayar da muke yi ba.” In ji shi.
Ya gode wa masoyansa da magoya bayansa, kana ya bukace su da su zauna cikin lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.