Babban rukunin rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya rawaito a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta aike da kayayyakin agajin gaggawa zuwa kasar Libya domin gudanar da ayyukan agaji ga bala’in da guguwa da ambaliyar ruwa ta haddasa.
Kayayyakin agajin da aka taso da su ta jirgin sama daga birnin Shanghai, sun hada da tantuna, barguna da sauran kayayyakin agajin gaggawa. Gwamnatin kasar Sin za ta kuma ba da tallafin jin kai na Yuan miliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 4.11 ga kasar Libya (Yahaya)