Wata kungiyar da ke goyon bayan gwamnan jihar Bauchi, wato Bala Abdulkadir Mohammed Vanguard (BAM-V), ta bukaci jam’iyyar adawa a jihar Bauchi, wato APC da dan takararta na zaben 2023, Ambasada Sadique Baba Abubakar da su rungumi kaddara gami da amincewa da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar wacce ta tabbatar da Bala Muhammad a matsayin halastaccen gwamnan jihar Bauchi.
Ita dai kotun sauraron kararrakin zaben mai alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a P.T Kwahar, ta kori karar da APC da dan takararta suka shigar da ke kalubalantar nasarar Bala Muhammad a karo na biyu.
- Shari’ar Zaben Gwamnan Bauchi: Sai Mun Ga Abin Da Ya Ture Wa Buzu Nadi – Dan Takarar APC
- Manyan Hafsoshin Sojin Nijeriya Da Suka Fafata Yakin Biyafara
Kungiyar BAM-V dangane da hukuncin, a wata sanarwar da darakta-janar, Kwamared Mohamemd Jibo Abubakar, ya fitar, ta taya Sanata Bala Muhammad murna bisa samun nasara a kotun, gami da bukatar ‘yan APC da sauran masu ruwa da tsaki a jihar da su hada hannu da gwamnatin Bala Muhammad domin ciyar da jihar Bauchi gaba.
Kungiyar ta bukaci ‘yan adawa da su jingine kalamansu na adawa tare da hada hannu da gwamna Bala Muhammad domin kyautata cigaban jihar, bunkasa tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kyautata jihar Bauchi da ma wajenta.
Kungiyar ta ce, tun lokacin da gwamnatin Bala Muhammad ta zo kan mulki a shekarar 2019, jihar ta samu ayyukan raya birane da karkara wanda hakan ne ya sanya jama’a da dama sake zaben gwamantin a karo na biyu.
Kungiyar ta nuna cewa hada kai da dukkanin bangarorin zai bai wa gwamnatin cikakken damar maida hankali wajen samar da ayyukan cigaba da bunkasa bangarori daban-daban domin kyautata rayuwar al’ummar jihar a kowane lokaci.