Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Gombe, ta kori karar da jam’iyyar ADC ta shigar a gabanta da take kalubalantar nasarar da Muhammadu Inuwa Yahaya ya samu na zama gwamnan jihar Gombe da mataimakinsa Manassah Daniel Jatau a karo na biyu.
ADC tana kalubalantar bayyana nasarar Inuwa Yahaya da INEC ta yi akan cewa an tafka magudi kuma Gwamna Inuwa da mataimakinsa sun gabatar da sunaye mabanbanta ga INEC.
- Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Sojoji Sun Ceto Wasu Karin Dalibai Mata 7 Na Jami’ar Tarayya Da Ke Gusau Jihar Zamfara
Kotun ta kori karar ne bisa dalilin cewa, dukkan korafe-korafen jam’iyyar ta gabanin zabe ce kuma shi mataimakin gwamnan yana da shaidar da doka ta lamunce masa neman takara.
Kotun ta kuma sanya kafa ta shure zarge-zargen da ADC ke yi na tafka magudi da cewa masu korafin sun gaza tabbatar da zarge-zargen da suke yi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp