Masana kimiyya daga kasashen Sin da Kenya, sun kaddamar da wani littafi na tsirran dake kasar Kenya a Nairobi, babban birnin kasar, wanda ke zama kundi na farko dake kunshe da tsirran da Allah ya horewa kasar da aka wallafa, tare da cike gibin dake akwai a fannin binciken albarkatun tsirrai a kasar.
Wannan wani aikin bincike ne na hadin gwiwa, wanda ya kunshi masana kimiyya daga cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin (CAS), da cibiyar nazarin hadin gwiwar Sin da Afirka (SAJOREC) da kuma gidajen adana kayan tarihi na kasar Kenya.
- Xi Ya Yi Kira Ga Lardin Zhejiang Da Ya Rubuta Sabon Babi Na Inganta Zamanantarwa Ta Sin
- Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau
A jawabinta yayin bikin, babbar darektar gidajen adana kayayyakin tarihi na kasar Kenya, Mary Gikungu ta ce kaddamar da littafin da ke bayani dalla-dalla kan tsirran dake kasar, zai bayyana kokarin kiyaye su da kokarin samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Tana mai cewa, littafin da suka kaddamar, yana da muhimmanci matuka, ganin yadda ya bayyana asalin tsirran kasar.
Gikungu ta jaddada cewa, ta hanyar hadin gwiwa da kasar Sin, gidajen adana kayayyakin tarihi na kasar Kenya sun samu damar kara karfin masu bincikensa, ta yadda za su kara inganta kiyaye muhalli daga tushe. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)