Bukayo Saka ya shiga cikin yan wasan Arsenal masu rauni yayin da Mikel Arteta ya tabbatar da jinyar dan kasar Ingilar.
Tauraron dan kwallon Arsenal Bukayo Saka ya samu rauni a wasan da aka yi a North London Derby a ranar Lahadi kociyan kungiyar Mikel Arteta ya bayyana.
Mikel Arteta ya ce Bukayo Saka ba zai iya buga karawar da Arsenal za ta yi da Brentford a gasar cin kofin Carabao ranar Laraba da kuma wasan da za ta yi da Bournemouth ranar Asabar ba.
Saka ya ji rauni a wasan karshe na wasan da Arsenal ta yi 2-2 tare da manyan abokan hamayyarta Tottenham ranar Lahadi a wasan Arewacin London.
A cikin taron manema labarai a ranar Talata Arteta ya bayyana wa manema labarai cewa akwai yiwuwar zai iya rasa wasan Bournemouth).
Arsenal za ta fara karawa da Brentford a gida a wannan Laraba yayinda Gabriel Martinelli, Leandro Trossard da Thomas Partey duka suke jinya.
Muna fatan ba wani babban abu bane Arteta ya fadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp