Kungiyar gamayyar kungiyoyin fasahar sarrafa kayan amfani gona (CONESAM), ta yi taron baje kolin fasahar sarrafa kayan amfanin gona a Jihar Kano.
Gamayyar kungiyar, karkashin shugabancin Alhaji Dahiru Saidu Gidado Wazirin Turakin Kano, ta shirya gagarumin taron baje kolin kayayyakin amfanin gona, wanda zai taimaka wajen samar bunkasar tattalin arzikin mata da sauran al’umma baki-daya, a cibiyar kyankyasar masa’antu da ke Kano, a makon da ya gabata.
- Kotu Ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Filato
- Kaunar Da Xi Jinping Yake Nuna Wa Gari, Dangi Da Kuma Al’ummar Kasa
Shugaban ya kara da cewa, yana daga cikin gudunmawar da wannan kungiya take bayarwa wajen kirkirar injinan da aka zo da su daga Kasashen Turai, wadanda suke sarrafawa tare da sayar da su cikin farashi mai rahusa. Sannan kashi 99 na injinan kyankyasar kwan kaji ne da kungiyoyin CONESAM ke sarrafa su.
Shi kuwa Babban Sakataran tsare-tsare da shirya taron, Shafiu Abdullahi Sunusi cewa ya yi, wannan taro ya samu nasara sosai musamman ganin yadda wannan kungiya ke samun nasasar kawar da talauci a tsakanin mata masu kananan sana’o’i.
Ita ma babbar jami’a mai kula da Jihohin Arewa ta Cibiyar Bunkasa Kananan Masana’antu da ta ‘RISA Project, Adamsmith International’, Ummi Rahama Shehu cewa ta yi wannan ziyara da shugaban wannan cibiya ya kawo daga Ingila a wannan lokaci, ya sa wannan taro ya yi matukar armashi; sannan kuma mata masu sana’o’i sun samu karfin gwiwa na taimaka wa wannan ‘RISA Project’ ta Afrika.