Mutane kimanin 300,000 cike da farin ciki ne suka taru a dandalin Tiananmen na birnin Beijing da safiyar jiya Lahadi, domin murnar cikar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin shekaru 74 da kafuwa, biki ne mai kayatarwa da jama’a a fadin kasar ke murnar zuwansa.
A bana, ranar 1 ga watan Oktoba, ita ce rana ta 3 na hutun kwanaki 8 a kasar Sin, wanda ya hada da hutun bikin tsakiyar kaka da na ranar kafuwar kasar, kuma tuni mutane da dama suka yi bulaguro bayan haduwa da iyalansu.
- ’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou
- Tawagar Masu Aikin Na’urar Binciken Duniyar Wata Mai Suna Chang’e 5 Ta Kasar Sin Ta Samu Babbar Lambar Yabo
A bana, wannan lokacin hutu na musamman ne domin shi ne irinsa na farko bayan annobar COVID 19, inda ake sa ran harkokin tafiye-tafiye da na sayyaya za su farfado har su zarce matakan da suke shekaru 3 da suka gabata.
A lardin Hunan dake kudancin kasar Sin, an yi tafiye-tafiyen da suka zarce miliyan 2.7 zuwa wuraren bude ido sama da 950 a ranar Asabar, karuwar kaso 71.6 kan na bara, yayin da kudin shigar da aka samu ya kai yuan miliyan 370, kwatankwacin dala miliyan 50.7, wanda ya nuna karuwar kaso 49.1 akan na bara.
An kunna fitilu masu alamta kishin kasa a gine-gine da tituna da muhimman wurare a fadin kasar, yayin da ake iya ganin tutocin kasar makale a jikin gine-gine da fitilun titi, har ma da motoci.
A yankin musammam na Hong Kong, an yi wasan tartsatsin wuta da misalin karfe 9 na yammacin jiya Lahadi, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan shekarar 2018. A shanghai kuwa, an ga jiragen ‘yan sanda masu saukar ungulu guda 3 na shawagi na musamman a sararin samaniya dake saman kogin Huangpu. Inda jirgin dake jagorantar sauran jiragen ke dauke da jar tuta mai taurari 5 yayin da sauran ke biye da shi gefe da gefe. (Fa’iza Mustapha)