Allah ya yi wa tsohon shugaban jami’ar Nsukka (UNN) da ke jihar Enugu, Farfesan Farfesoshi Umaru Shehu rasuwa.
Fitaccen Farfesa ne a fannin likitanci wanda ya rike mukamai masu yawa a jami’o’i da dama da suka hada da jami’ar Nsukka (UNN) Enugu, Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria, da Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), kuma shugaba ne a kwamitin gudanarwa na Cibiyar Nazarin Halittar Dan Adam ta Nijeriya.
- Jama’a A Fadin Kasar Sin Na Bikin Ranar Kafuwar Kasar Yayin Da Suka Shiga Lokacin Hutu Mai Tsawo
- Cire Tallafin Fetur: Zulum Ya Amince Da Ba Ma’aikatan Jihar Borno Rancen Naira Biliyan 2
Wata sanarwa da kungiyar dattawan Borno ta fitar ta hannun Sakatarenta, Dakta Bulama Gubio, a ranar Litinin ta sanar da rasuwar Farfesan a ranar Litinin.
Farfesa Shehu, wanda ya rasu yana da shekaru 97 a duniya, shi ne ya kafa gidauniyar tarihi da al’adu ta Kanem Borno, kuma shi ne wanda ya kafa kungiyar dattawan Borno.
An haifi Farfesa Shehu ne a ranar 8 ga watan Disamba, 1930 a Maiduguri a jihar Borno. Ya yi makarantar farko a Maiduguri daga 1935 zuwa 1940; Makarantar tsakiya a Maiduguri daga 1941 zuwa 1943; Kwalejin Kaduna daga 1944 zuwa 1947; Kwalejin Jami’ar Ibadan daga 1948 zuwa 1953; sannan Jami’ar Liverpool da ke Birtaniya tsakanin 1953 zuwa 1956, da 1966 zuwa 1967.
Farfesa Shehu ya samu digirin farko a fannin likitanci a Jami’ar Landan, kuma shi ne Babban Editan Jaridar Likitanci ta Birtaniya.
Sanarwar ta kara da cewa, za a yi jana’izar Farfesa Shehu a yau Litinin a gidansa da ke Old GRA, Maiduguri, babban birnin jihar Borno.