• English
  • Business News
Friday, May 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
1 month ago
in Dausayin Musulunci
0
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Fahimtar Alkur’ani Mai Girma Da Irin Wayewar Kan Zamaninmu

Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Masu karatu barkanmu da Sallah, da fatan mun yi bukukuwan Sallah lafiya. Allah ya karba mana ibadunmu. Allah ya gafarta wa marigayanmu. Allah ya zaunar da kasarmu da duk kasashen musulmi lafiya, Allah ya kwatar wa Falasdinawa hakkinsu, ya karya duk masu zaluntarsu Albarkar Annabi (SAW).

Bayan haka, daga wannan mako. Za mu fara kawo muku wasu darussa da wasu masu bibiyarmu suka zakulo daga tafsirin Alkur’ani mai girma da muka gabatar a Kaduna, a Zawiyyarmu ta Ahlul Faidhati Mai Diwani Group. Ba ni Isma’ila ne na rubuta ba, masu bibiya ne suka rubuta daga darussan da suka koya cikin tafsirin. Ga sakonnin kamar haka:

  • Karin Haraji: Amurka Ta Debo Ruwan Dafa Kanta
  • LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci

– Mu Fahimci Alkur’ani Da Irin Wayewar Zamaninmu

Assalamu alaikum, Shehu Isma’ila Umkar Almadda (Mai Diwani), ina mika sakon ban gajiya na gabatar da tafsirin Aklur’ani mai girma a watan Ramadan. Da fatan an yi Sallah lafiya, Allah ya karba mana ibadunmu amin. Akramakallah, Allah ya saka maka da alkhairi. Hakika na karu da shimfidar da ka yi mana a ranar tafsirinka ta farko wadda ka bude a Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group, ranar Laraba 26 ga Fabrairun 2025.

Labarai Masu Nasaba

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)

Na ji dadi da yadda ka yi kira ga sauran Malamai da su zama masu kwadaitar da neman Ilimi a kowanne fanni, sannan su kaurace wa furta haramci a kan abubuwan da Shari’a ba ta yi haramci a kai ba. Tabbas, ayoyin Alkur’ani suna nan kamar yadda aka saukar kuma ba za su sauya ba har duniya ta nade, amma fahimtarsu tana sauyawa daidai da zamani, don haka, bai dace a yi watsi da kimiyya da fasahar zamanin nan ba da ake ganin na turawa ne kawai, matukar ba a samu fiye da tasu ba.

Akramakallah, gaskiya ne, ya dace Malamai su rika ba da fatawa da ta yi daidai da zamaninsu da kuma fahimtar da al’ummar Musulmai Isharori na Alkur’ani, domin kamar yadda ka yi bayani, cewa, Suratul Bakara wacce ake ce mata “Surarar Saniya”, ba ta tsaya a kan saniya kawai ba, tana nufin Fadin Ilimi gaba dayansa, domin babu wani Ilimi a Alkur’ani face sai an ga wani abu na bayaninsa a cikin Suratul Bakrah.

Haka nan, misalin da ka bayar na cewa, a wannan zamanin Suratul Ankabuti, da ake fassara ta da “Surar Yanar Gizo-Gizo”, ya fi kyautatuwa a wannan lokacin a fassara ta da “Surar Website”.

Kazalika, Suratun Namli, da ke nufin “Surar Tururuwa”, ita kuma tana koya mana bin tsari, da abun da yake mai amfani da mara amfani da dai sauransu.

A gaskiya, na ji dadin karuwa da wannan ilimi daga tafsirin, Allah ya saka da alkhairi, ya kara ilimi da hikimomi na fahimtar Alkur’ani mai girma, amin.

Sako daga Ibrahim Sulaiman Muhammad

-Nau’o’in Halittar Allah Da Abubuwan Da Suka kunsa Hikima Ce Babba

Salam. Ya Sayyadi muna gabatar maka da gaisuwa ta amincin Allah, da fatan an yi Sallah lafiya. Allah ya saka muku da alkhairi. Bayan haka, muna mika godiya da irin karatun da muka ji game da hikimomin da Allah ya zuba a cikin dukkan sassan halitta, ta yadda komai ya zama littafi na ilimi mai zaman kansa. Hakika mun karu da bayani dalla-dalla da ka yi a game da matakan ilimi a matsayin KITABU, da abubuwan da suke kunsa.

A yanzu na fahimci cewa, hatta ruwan sama littafi ne saboda fannoni na haduwar ilimi ke samar da shi da kuma amfanin da yake yi. Don haka, idan mun sa lura, za mu ga cewa duk wani abu samamme yana zaman littafi ne sai dai ban da samuwar RABBUL IZZATI.

Allah ya saka muku da alkhairi da wannan wayar da kai da kake wa al’ummar Musulmi. Allah ya kara fahimta mai yawa ta isar da sakon Annabi (SAW).

Sako daga Abdullahi Jejiba Kaduna

-Alkur’ani Ba Shi Da Shamaki, Tabbas Ya Game Ko Ina Kuma Na Kowa Da Kowa Ne

Salamullahi alaikum. Ya Shehi, muna mika ziyararmu ta musamman, Allah ya saka muku da alkhairi. Farin ciki ya sa ni aiko da wannan sako a kan bayanin da ka yin a cewa, Alkur’ani mai girma littafi ne na duk duniya da Allah ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da shi, ba na musulmi ba ne kawai. Mun fahimci cewa duk wata kwarewa da ake takama da ita a duniya tana nan a cikin Alkur’ani kuma kowa zai iya amfana da Alkur’ani ya samar da ci gab awa kansa da garinsa da kuma duk duniya ma baki daya.

Haka nan, mun kara fahimtar ma’anar littafi da yadda ake fahimtar ilimomi da ke kunshe a karkarshin sunan littafi da harshen larabci na “Kitabu” ko “Khaddu” da sauran kalmomi irin su “Kataba”, musamman wadanda suka zo a cikin Alkur’ani mai girma. Bayanin da ka yi dangane da batun abubuwan da suka shafi “Hukunci” da wadanda karfin ikon hukunci yake hannunsu sun kara wayar mana da kai a game da yadda aka cakuda abubuwa a cikin addinin nan namu daga wadanda suka biye ma son ransu. Haka nan karin hasken da ka yi game da abin da ya shafi “Mutashabihun” da ma’aunin da ake ganewa sun kara mana ilimi sosai. Wallahi tafsirinka na rana ta uku ya ilmantar da mu sosai, Allah ya saka muku da alkhairi.

Sako daga Usman Yahaya Nuhu Goron Dutse.

-Manzon Allah (SAW) Ya Wayar Wa Duniya Kai A Kan Tsarin Zaman Madina

Salam. Ya Shehi, muna muku barka da ganin lokacin watan Azumin Ramadan na bana. Da fatan Allah ya karba mana da falalarsa. Allah ya kara muku koshin lafiya, ya kara hikima da basira ta wayar da kan al’ummar Musulmi. Hakik ana ji dadi da bayanan da na samu a cikin Tafsirinka na bana na rana ta hudu wanda muka fahimci Manzon Allah (SAW) ne ya fara kawo wayewar kai game da tsara daftarin hukuncin, watau ‘Consultation’ a duniya, a zamantakewar birnin Madina. Mutane da yawa suna wa tsarin zamantakewar jama’a bahaguwar fahimta, to amma wannan ya kara nuna mana yadda addinin Musulunci ya koyar da zama na birni wanda duk wani mai tutiyar wayewa zai fahimci daga tsarin Musulunci ne aka koya.

Har ila yau, hukunce-hukuncen da ka kawo na kyawawan dabi’u guda 38 da Allah ya kawo a cikin Alkur’ani, da yadda suke a cikin daftarin hukuncin na zamantakewa a Madina da Manzon Allah (SAW) ya tsara, wanda ya bai wa mace hakkokinta da tabbatar da tausayi da kuma girmama rayukan bil’adama, sun isar da kyakkyawan sako ga duk wani mai son sanin gaskiyar tsarin addinin Musulunci.

Mun kuma karu da bayanin da ka yi a kan hukunce-hukunce guda goma da Annabi  Isah (AS) ya dauka daga cikin Attaurar Annabi Musa (wasaayal Ashri) wadanda dukkansu hukunce-hukunce ne na hani masu zafi.

Ya Shehi, muna godiya da tsokacin da ka yi a kan hukunce-hukunce talatin da takwas (38) da ake kira da “Muhkamatu”, wadanda suka zo a cikin ayoyi takwas na Alkur’ani wadanda dai duk su ne na farko da suke a kan allon Attaura.

Muna kuma godiya da wayar mana da kai a game da cewa, babu kashe-kashen rayukan mutane da sunan addini a Musulunci, kasancewar duk yakokin da Annabi ya yi da sahabbansa, ya yi su ne domin kariyar kai ko kuma mayar da martani ga masu bore daga cikin al’umma.

Ya kamata lallai malaman addini da su gyara wa’azinsu game da hukuncin kisa a addini domin samun tabbataccen zaman lafiya, da yin kira ga al’umma a kan aikata kyawawan ayyuka nagari da kuma guje ma munanan ayyuka na duk nau’o’in alfasha. Allah ya saka muku da alkhairi. Mun gode.

Sako daga Aminu dahiru Rafindadi

-Mun Fahimci Bambancin Zaman Birni Da Na kauye, Akramakallah

Assalamu alaikum, Allah gafarta Malam, Allah ya saka maka da alkhairi. Tabbas tafsirinka na rana ta biyar ta fayyace mana abin da ya sa ake samun ci gaba a zaman birni saboda kasancewar nan ne matattarar mutane daban-daban don haka ake samun habaka da samun ci gaba irin na zamani saboda rungumar sauyin zamani. Sabanin kauye wanda su ba su yarda da kawo sauyi ko bakon abu. Tabbas, karamin gari ba ya rungumar sauyin zamani, yana nan a kan yadda yake duk da kuwa dimbin alkhairai da zamani ke tahowa da su, saboda haka ne ma ya sa, sai ka ga hatta mazauna garin sun fara ficewa, har wata rana a nemi kowa a rasa ko kuma a nan ne aka fi musunta sakon Ubangiji har a kai wani lokacin da Allah yake halakar da kauyen.

Halayyar kauye na tattare komai da kin yarda da sabbin abubuwa na ci gaba ko kin amincewa da kishiya tamkar musharaka ce da shirka, domin Allah Ta’ala ne ba ya son kishiya. Dole idan aka samu duhun kai irin wannan sai jarrabawa ta hau kan masu yi.

Mun gode wa Allah, da Shari’ar Annabi Muhammad (SAW), ta zama ta duniya ce baki daya (International), don haka ta zama mai sauki saboda duk abin da ya shafi duk duniya, ba wata al’umma daya ba, dole ne ya zama mai sauki.

Shari’ar Manzon Allah (SAW), Rahama ce ga dukkan Al’umma. Don haka, ya dace Malamai su rika kwadaitar da al’ummar Annabi (SAW) Rahamar Ubangiji, da kore haddi da Shubuha, domin Allah Ta’ala da ya sanya dokoki masu matukar wuya kawo shaidun haddin Zina wacce bulala ce sakamakonta, ba zai zama hikima ba kuma a ce ya bar haddin zubar da jini a fili sakaka.

Muna godiya da tarihin da ka bayar na kafuwar dimokuradiyya a Musulunci da aka faro daga kan khalifancin Sayyidina Aliyu (Karramallahu Wajhahu). Allah ya kara fikira da fahimta Albarkar Annabi (SAW).

Sako daga Abdullahi Mustapha Bauchi.

Alhamdu lillah, duk muna godiya da sakonninku masu bibiyarmu, Allah ya saka wa kowa da alkhairi. In sha Allahu za mu kawo ragowar sakonnin a gaba. Mun gode.

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Dausayin MusulunciTafsiri
ShareTweetSendShare
Previous Post

Masarautar Hadejia Ta Raba Zakka Ta Fiye Da Naira Biliyan 1 Ga Mabuƙata 

Next Post

Dubban Jama’a Sun Sallaci Gawar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Related

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Dausayin Musulunci

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

2 weeks ago
Ramadan
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)

3 weeks ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

4 weeks ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci

1 month ago
Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah
Dausayin Musulunci

Azumi Ya Dara Wa Sauran Ibadu

2 months ago
Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah
Dausayin Musulunci

Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah

2 months ago
Next Post
Dubban Jama’a Sun Sallaci Gawar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Dubban Jama'a Sun Sallaci Gawar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

May 15, 2025
Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

May 15, 2025
Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

May 15, 2025
Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

May 15, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

May 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

May 15, 2025
An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

May 15, 2025
HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

May 15, 2025
Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

May 15, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.