Majalisar dattawa za ta yi bincike kan zargin daure ‘yan Nijeriya sama da 250 a gidan yari tare da kashe su a kasar Habasha.
Binciken ya biyo bayan amincewa da kudirin da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Simon Mwadkwon, (Filato ta Arewa) da Sanata Victor Umeh (Anambra ta tsakiya) suka gabatar.
- Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Sanata Ta Tsige Sanata Jibril Isah Na Mazabar Kogi Ta Gabas
- Manyan Batutuwa 7 Da Za Su Turnike Zauren Majalisa Bayan Dawowa Hutu
A wani kudiri da aka gabatar mai taken: “Bukatar gaggauta gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa ‘yan Nijeriya sama da 250 a kasar Habasha ba bisa ka’ida ba,” ya bukaci majalisar dattawa da ta hada kai da gwamnatin tarayya domin kafa wani kwamitin gaggawa da zai ziyarci kasar Habasha da nufin jin ba’asin abinda ke faruwa da yan Nijeriya a kasar.
Har ila yau, kudirin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta umurtar ofishin jakadancin Nijeriya da ke kasar Habasha da ta hada kai da tawagar kwamitin majalisar dattawa mai kula da al’amuran kasashen waje domin nemo mafita kan halin da ‘yan Nijeriya suka tsinci kansu a kasar Habasha.
Sanata Mwadkwon a cikin jawabinsa, ya yi nuni da cewa, a wani faifan bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta, ya nuna cewa, an tsare ‘yan Nijeriya a gidan yari mafi girma na kasar Habasha kuma suna cikin hadari mai tsanani wanda ya bukaci a gaggauta shiga tsakani da kuma gudanar da bincike sosai kan zargin.
Sanatan ya koka da cewa, bai dace hakan na faruwa a tsakanin kasashen Afirka ba duba da yadda ake ta kiraye-kirayen hadin kai a tsakanin kasashen.