Wannan wata tattaunawa ce da muka yi da Kwamishiniyar ma’aikatar Jin ƙai da Walwalar Al’umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim (Garkuwar Marayun Zazzau), wacce kuma ta kasance jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi da son taimaka wa al’umma. Wanda wannan ne ya sa jama’a da dama ke ganin cewa tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafa wa waɗanda aka zalunta, zawarawa da marayu, da kuma jajicewarta wajen ƙwatar ‘yanci ga ƙananan yara maza da mata waɗanda ake yi wa fyaɗe, na wasu daga cikin dalilan da suka sanya ta kafa Gidauniyar Arridah, inda mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana.
Jama’a da dama na ganin cewa zai iya kasancewa bisa la’akari da irin waɗannan abubuwa nata, da kuma zaman ta ‘yar siyasar da ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin Mai girma Gwamna Uba Sani ya cimma wannan matsayi, ya sanya ta hawa wannan kujera ta Kwamishina, wanda kuma aka ba ta fagen da ta fi fice a kai.
A cikin wannan tattaunawar, Hajiya Rabi ta bayyana mana inda ta sanya gaba a wannan ma’aikata, ta kuma yi bayanin abubuwan da ke gaban ta da kuma wasu bayanai masu ilimantarwa. A dai biyo mu a sha labari.
Ga yadda tattaunawar ta kasance;
Za mu so ki yi mana bayanin inda aka dosa a cikin wannan tafiya ta wannan ma’aikata da kike jagoranta?
A gaskiya, kamar dai kullum irin, wannan tambaya tana buƙatar nazari sosai, ganin cewa wannan ma’aikata ta harkokin jin ƙai da kuma walwalar al’umma ta tara fannoni da dama. Abubuwan da mu ka saka a gaba su na da yawa.
Misali, ka ga akwai ɓangaren da ya shafi matasa, akwai ɓangaren da ya shafi mata, sannan muna da ɓangaren da ya shafi walwalar yara da mutane masu naƙasa da kuma dai sauran ɓangarori da dama.
Don haka ma’aikatar tana da girma sosai ganin yadda ta ƙunshi waɗannan ɓangarori, wanda hakan ya sa idan za mu aiwatar da wani abu, sai mu duba dukka ɓangarorin. Mu na da kuma ɓangaren da ya shafi karkara da birane.
Akwai abubuwan da mu ke kallo da dama, irin su; yaƙi da cin zarafin ƙananan yara, maA da mata, wanda mu ke ɗaukar mataki idan aka ci zarafin su ta ɓangaren wuraren aiki, auratayya, ko kuwa yara kanana ne da ake yi wa fyaɗe, ko kuwa abin da ya shafi yaran da su ke samu matsaloli, har abin da ya shafi makarantun tsangaya, da almajirai da mutane masu fama da naƙasa.
Irin waɗannan abubuwan duk wanda aka ɗauko mu na da tsarin sa, duk da cewa gwamnatin nan ɗaya da ta baya, amma duk tsarin iri ɗaya, ci gaba ne ake samu, sai dai ɗan ƙarin da ake yi na wasu abubuwa. Abubuwan da mu ka zo muka taras, mun ci gaba da yi ne, sai dai mu ke ƙara faɗaɗa su domin al’umma su amfana.
To, waɗanne hanyoyi ne yanzu ku ka ƙara don ganin cewa wannan tsari na ku ya cimma mabuƙa, ba wasu daban ba, musamman wajen rabon kayan rage raɗaɗin janye tallafin man fetur da gwamnati ta bayar?
Kamar maganar da Mai Girma Gwamna Jihar Kaduna, Uba Sani yi yi a kan batun rabon kayan tallafi don rage wa al’umma raɗaɗin cire tallafin man fetur, to kafin Gwamnatin Tarayya ta ayyana bayar da wani kaso ga al’umma na tallafi, akwai tsare-tsaren da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi, wansa kuma ta yi nisa akai na fara tanadar abinci daga rumbunan ta don bai wa jama’a, sai kuma Gwamnatin Tarayya ta ayyana za ta bai wa kowacce jiha kuɗaɗe, wanda Alhamdulillah Jihar Kaduna tana cikin jihar da ta samu waɗannan kutaɗe, duk da kaso arba’in da uku na kuɗin za a mayar, sauran kuma bashi ne ga jihohi, sauran kaso hamsin da bakwai gudunmawa ne ga al’ummar wadanan jihohin.
To, waɗannna kuɗaɗe an yi amfani da su ne wajen sayen kayan abinci, wanda Mai Girma Gwamna ya faɗi hasafin kayan abinci da za a saya na Naira biliyan ɗaya da Naira miliyan ɗari tara da arba’in da wani abu, miliyan sittin da ’yan kai ne zai rago na bayar da tallafin tsabar kuɗi ga gidajen marayu ko mutane masu naƙasa, tsofaffi da matan da mazajen su suka rasu.
Amma a rabo na biyu, ana sa ran za a bai wa manoma taki, za a tayar da Jirgin kasa mai zirga-zirga a cikin jihar, da kuma shiga mota kyauta da abubuwa da dama dai na more rayuwa. Amma a wannan karo na farko, abinci ake da buƙata, wanda mutane za su amfana.
Sannan Alhamdulillah, wannan ma’aikata mu na da ruwa da tsaki a harkar rabo, duk da cewa ita Mai Girma Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe Sabuwa, ita ce shugabar wannan kwamitin da gwamna ya naɗa, ita ke jagorantar mu tare da ’yan ƙungiyar ƙwadago, ƙungiyar ‘yan kasuwa, ƙungiyoyin mata, ƙungiyoyin masu naƙasa da dai sauran ƙungiyoyi, duk an gayyace su don su faɗi yadda za a raba wa al’umma wannan tallafi.
An tsara rabon wannan tallafi ne a kananan Hukumomi 23 da Jihar Kaduna ta ke da su, wanda za a kai wa waɗannan kananan Hukumomi waɗannan kaya don rabo, wanda ake sa ran mutum miliyan ɗaya da ɗari da hamsin ne za su amfani da wannan kaya. Kuma ba a taba rabon kaya masu yawa kama irin wannan ba, duk rabon da aka yi a baya.
A yadda aka tsara ma, mutum zai iya ci na kwana goma ko mako ɗaya a gidansa. Idan ka kai su kananan Hukumomi, sai an kira Liman, Fasto, mai Unguwa, masu ruwa da tsaki, masu naƙasa da matasa, duk a gaban su za a raba na gundumomi. Ba a yarda Ƙaramar Hukuma ta tara mutane ta raba kayan ba, sai kowanne gunduma ya zo ya ɗauki na shi. Su ma idan suka kai wajen su, ba a yarda su raba ba sai sun kira kowanne yanki sun ba su na su, su kai garinsu su raba. A halin yanzu ana duba waɗanda su ka fi kowa buƙata ne, ba a fara zuwa ga ma’aikata ba.
Daman kin yi fice wajen kare haƙƙin masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda aka zalunta, to yanzu Allah Ya ba ki mulki, shin me ki ke yi na ganin cewa an hukunta masu irin waɗannan ɗabi’u?
Kamar mutum ne a ce za shi kitsu sai aka haɗa masa da masilla’, daman can mu na yi a matsayinmu na ’yan sa-kai, to yanzu kuma aikin ne aka ɗauka aka ba mu a gwamnatance, kuma wannan ma’aikata ne ke da alhakin irin waɗannan abubuwan na kare haƙƙoƙin yara da mata a duk faɗin Jihar Kaduna.
Zan yi ƙoƙarin ganin cewa mun san waɗannan matsaloli da kuma inda su ke, mun san kuma hanyoyin magance su, wanda a da sai dai mu yi kira ga gwamnati ta yi.
Yanzu zan yi amfani da sanayya da wasu hanyoyi don gano tushen matsalolin, da kuma yadda za mu bi su don a rika samun hukunci a cikin lokaci, duk da cewa ba ni ba ce mai yin hukunci, mu na mu bibiya ne. Mun yi haɗin gwiwa tare da ma’aikatar shari’a da hukumar ’yan sanda.
A karshe, waɗanne ƙalubale ne ku ke ki ka tarar a wannan ma’aikata?
Duk wani abin ci gaba ba ya rabuwa da ƙalubale. Tun da mu ne ake kawo wa kuka, to mu kuma sai dai mu kai kukanmu wajen Allah. Abin da kawai za mu iya cewa shi ne, ba ma son iyaye, Sarakuna da masu unguwanni su na kashe kes a fadar mai unguwa, duk abin da ya zama babban laifi, a bar shi ya fito a yi hukunci don ya riƙa zama izina ga masu burin aikata irinsa.
kalubale na biyu shi ne ƙyama da ake nunawa ga waɗanda aka zalunta, wanda idan an ce su zo a taimake su, sai su ce a’a, saboda za a yayata su, jama’a su ƙyamace su. Bai kamata al’umma su ƙyamaci waɗanda aka zalunta ba, azzalumi ne abin ƙyamata. Muna fatan al’umma su riƙa taimaka wa waɗanda aka zalunta.