Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin hukumar kwastam ta Nijeriya ya umurci hukumar da ta yi gyara akan tsarin tantance adadin abin hawa (Duti/VIN) ko kuma a dakatar da tsarin baki daya.
Hakan na kunshe ne cikin rahoton da kwamitin Majalisar ya gabatar wa Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), Kanal Hameed Ali (Rtd), a Abuja ranar Litinin.
Duti, tsarine da Hukumar kwastam ke amfani da shi wajen karbar harajin motocin da ake shigowa da su cikin Nijeriya, bisa la’akari da shekarar da aka kera su.
Rahoton da shugaban kwamitin, Leke Abejide ya gabatar, an samo rahoton ne bayan ganawar shugaban da jami’an kwastam da ke shiyya ta daya (A), Legas, a yayin wata ziyarar sa-ido da ya kai wa hukumar a yankin.
Da yake gabatar da rahoton, dan majalisar ya bayyana cewa, kwamitin ya lura da yadda tsarin VIN yake tayar da kayar baya ga masu shigo da kaya masu lasisi da sauran masu ruwa da tsaki da ke aiki a tashoshin ruwan kasar nan.