Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samar da hanyar jin-kai ga dalibai 66 ‘yan asalin Jihar da aka dawo da su gida daga Sudan.
Gwamnatin Jihar Zamfara ce ta tura Dalibai 66 karatu Sudan, wadanda kuma ba su kammala karatunsu ba aka dawo da su sakamakon yakin da ya kaure.
A wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa Kwamishinan Ilimi ne ya yi karin haske ga Majalisar Zartaswar Jihar a zamanta na ranar Litinin.
Ya kara da cewa, dalibai 14 cikin 66 da aka dawo da su daga Kasar ta Sudan suna gab da rubuta jarabawar karshe a fannin Jinya, kafin farawar yakin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A watan da ya gabata ne Gwamna Dauda Lawal ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Zamfara da ta kulla yarjejeniya da hukumar gudanarwar Jami’ar Sudan domin ganin dalibai 14 ‘yan salin Zamfara sun iya rubuta jarabawarsu ta karshe a Nijeriya. Wanda a tsarin jami’ar ta Sudan, Nijeriya ba ta daga cikin cibiyoyin da za a iya yin wannan jarabawa a fadin duniya. Amma bisa jajircewa irin ta gwamnatin Zamfara ya sa suka aminta.
“Haka kuma Gwamnatin ta Zamfara ta roki Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato da ta bada Asibitin Kwararru na Jami’ar domin a gudanar da wannan jarabawa. Wanda kuma Jami’ar ta Dan Fodio ta amince.
“Cikin tausayawa da jin kai irin na Gwamna Dauda Lawal ne ya dauke nauyin kudin jirgi, masauki da duk wata dawainiya ta malamai uku da suka zo Nijeriya daga Sudan don gudanar da wannan jarabawa. Wannan kuwa duk na daga cikin irin kishin da gwamnan yake da shi ga harkar ilimi ne.
“An gudanar da wannan jarabawar ne ga daliban Zamfara 14 daga ranar 23 ga watan Satumba zuwa 30 ga watan Satumbar 2023.
“Gwamnatin ta Zamfara tana ci gaba da bin duk matakan da suka dace don ganin an kammala samar da guraben karatu ga ragowar ɗalibai 52 da suka dawo.
“Tuni Ma’aikatar Ilimi ta Zamfara ta kammala daukar bayanan dalibai 32 cikin 52 da suka rage, wadanda suka kammala duk wata tantancewa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya dake Abuja.
“Da zaran Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta kammala tantance daliban, za a samar musu da guraben karatu a mabambantan jami’o’i.”