Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya Charles Onunaiju, ya bayyana a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar, ta sanya sabon ci gaba a Najeriya, kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka, ta kuma samarwa kasar karin damammakin shiga harkokin tattalin arziki na duniya.
Onunaiju ya yi imanin cewa, kara shiga a dama da ita wajen raya shawarar cikin hadin gwiwa, zai sa Najeriya ta samu karin damammaki na samun darajar kasa da kasa, da kara aza harsashin bunkasa masana’antu. Yana mai cewa, inganta gina ababen more rayuwa a karkashin shawarar, sannu a hankali zai taimaka wa Najeriya canza fifikon da take da shi a fannin albarkatu da yawan jama’a zuwa ga ci gaban masana’antu.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp