Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, a ranar Talata ta kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a muhimmancin karban katin shaidar yin zabe na dindindin (PVC) ga mazauna birnin tarayya Abuja.
A gangamin na kan hanya da suke yi wa jama’a, su na nuna musu gayar muhimmancin zuwa don yin rijistan katin zabe ga dukkanin wadanda suka cancanci hakan ko kuma zuwa domin karba ga wadanda suka yi rijistan tare da jawo hankalinsu da su jefa kuri’ar nasu ga jam’iyyar PDP.
Sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC a Nijeriya, Hon Debo Ologunagba, da shugabar mata na jam’iyyar ta kasa, Farfesa Stella Effa-Attoe, sune suka jagoranci gangamin da aka gudanar a Abuja.
Masu gangamin sun yi ta kiran jama’a da su yi umumu su fito domin zabar jam’iyyar PDP, suna masu nuna musu cewa muddin idan mutum fa baida katin zaben babu abun da zai iya yi wajen zaban wanda yake so, don haka ne suka nemi jama’an da su yi hakan domin basu dammar shiga manyan zabukan da ke tafe.