• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Zan Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba – Gwamna Lawal

by Leadership Hausa
2 years ago
Sulhu

Gwamnan Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kauracewa duk wani batun sulhu da barayi a fadin Jihar Zamfara.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya halarci taron wa’azi na mako-mako da aka saba gudanarwa a Gusau, inda ya hori Malaman Addini da su kasance masu riko da gaskiya.

  • Yadda Kwankwaso Da Abba Suka Jagoranci Auren Gatan Mutum 1,800 A Kano
  • Nijeriya Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur A 2024 —Kyari

Wata takardar sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce wannan taron wa’azin mako an kwashe shekaru ana gudanar da shi, kuma wannan shi ne karo na 1,179.

Ya kara da cewa, gwamnan ya yi kira ga dukkanin shugabannin bangarorin al’umma da su kasance masu gaskiya a dukkanin al’amuransu, tare kuma da yawaita addu’ar wanzuwar zaman lafiya a Jihar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamna Dauda Lawal, a yayin da yake jawabi a wurin taron wa’azin mako a Gusau, ya bayyana irin hatsarin da yake tattare da yin sulhu da ‘yan bindiga, inda ya ce, babu abin da sulhun zai haifar sai karin karfi a gare su, tare da ci gaba da jefa al’umma cikin hatsari.

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

“Ya bayyana cewa dole ne a fuskanci gaskiya, domin kuwa wadannan lalatattun sun nuna cewa ba wai sulhun suke son yi da gaske ba, saboda sun kasance masu saba alkawari. Babu abin da ya rage face a durfafe su da karfin tsiya.

“Gwamna Lawal ya kuma yi kira ga shugabanni, sarakuna da malamai da su rika fadin gaskiya komi dacinta, ba tare da la’akari da wa ta shafa ba, komi dadi ko rashin dadinta.

“Ya yi kira ga shugabannin siyasa da al’umma da su muhimmanta lamarin tsaron jihar gaba da siyasa, domin zaman lafiyan Zamfara shi ne gaba da komi.”

Tun farko dai, a nashi lakcar, shugaban Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Zamfara, Sheikh Ahmad Umar Kanoma, ya yi dogon jawabi a kan muhimmanci sulhu, inda ya kawo sharudan da addinin musulunci ya gindaya wurin yin sulhu, da kuma yanayin da bai yiwuwa a yi sulhu a addinance.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna
Labarai

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
Labarai

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
Labarai

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Next Post
Kasashe 10 Da Ke Kan Gaba A Mallakar Ma’adanin Gwal A Afirka

Kasashe 10 Da Ke Kan Gaba A Mallakar Ma’adanin Gwal A Afirka

LABARAI MASU NASABA

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.