Gwamnatin Jihar Kano Karkashin jagorancin, Abba Kabir Yusif ta kaddamar da auren zawarawa 1,800 wanda aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na Gidan Sarkin Kano.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, suka jagoranci daurin auren.
- Wike Ya Yi Wa EU Wankin Babban Bargo Kan Zaben 2023
- Nijeriya Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur A 2024 —Kyari
Haka zalika, an daura da auren sauran zawarawan a kananan hukumomin Jihar Kano 44, wanda aka gudanar a masallatan Juma’a na shelkwatar kananan hukumomin.
Da yake Karin haske jim kadan da daura auren zawarawan karamar hukumar Kunchi, babban limamin karamar hukumar Kunchi, Imam Gwani Nazifi Abubakar, ya taya angwaye da amaren murnar sannan ya bukace su da su zauna da juna cikin aminci da amana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp