Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana aniyarsa ta ganin ya zamanantar da gidan talbijin ɗin Gwamnatin Tarayya (NTA) ta yadda zai yi goyayya da sauran manyan tashoshin talbijin da ake ji da su a duniya.
Idris ya ce zai ɗora kan shirin maida NTA bisa tsarin aiki cikin sauƙi kuma a zamanance, wato ‘Digital Switch Over’, wanda Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC) ke kan yi.
- Tsohon Minista Alhaji Bello Maitama Yusuf Ya Rasu Yana Da Shekaru 76 A Kano
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Muhimmanta ‘Yancin ‘Yan Jarida – Minista
Ministan ya yi wannan albishir ne a lokacin da ya kai ziyara a hedikwatar NTA, a wani rangadin duba hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa da ya ke yi, a ranar Talata.
Ya ce: “Dukkan mu dai mun san irin rawar da NTA ta taka da kuma gudunmawar ta wajen isar da saƙwanni da nishaɗantarwa ga ƙasar mu tsawon shekaru da dama. NTA ta na kan gaba wajen sanar da labarai da ɗumi-ɗumi masu muhimmanci ga ƙasa, sannan ta shahara wajen nuna kyawawan al’adun mu daga ɓangarorin ƙabilun ƙasar nan daban-daban.”
Ya yi tsinkayen cewa aikin babbar kafar yaɗa labarai kamar NTA abu ne da ya zama hantsi leƙa gidan kowa. Kan haka ne ya jinjina wa tashar dangane da yadda su ke gabatar da sahihan labarai, waɗanda ya ce sun taimaka sosai wajen isar da kyawawa kuma ingantattun bayanai ga ‘yan Nijeriya.
Minista ya ƙara da cewa batun wayar da kan jama’a shi ne babban ginshiƙin da zai ƙarfafa ma’aikatar sa. Kan haka ne ya ce NTA za ta taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa kyawawan ɗabi’un wayar da kan jama’a, waɗanda ma’aikatar sa za ta bijiro da su domin ɗora ƙasar nan kan nagartacciyar turbar cigaba mai ɗorewa.
Idris ya ce ya na fatan ganin ya bunƙasa NTA wadda ko bayan saukar sa daga mulki ya kasance ta na goyayya kafaɗa da kafaɗa da manyan gidajen talbijin ɗin da ake tinƙaho da su a duniya yanzu haka a ƙarni na 21.
Ya kuma yi alƙawarin zai samar wa NTA da dukkan kuɗaɗen da ta ke buƙata domin ganin cewa ayyukan ta na tafiya daidai, ba tare da tsaiko ko wata tangarɗa ba.