Eseme Eyiboh, kakakin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce babu hannun shugabansa a tsige Sanata Elisha Abbo mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dokokin kasar nan.
“Sakamakon shari’ar kotu na aiki ne na tantance gaskiya da hujjoji,” in ji Eyiboh a cikin wata sanarwa sa’o’i kadan bayan da korarren Sanatan ya yi ikirarin cewa an tsige shi ne saboda rashin goyon bayan takarar shugaban majalisar dattawa na Akpabio a farkon watan Yuni.
- Ranar Abinci Ta Duniya: Mata Manoma Zasu Samu Tallafin Aikin Gona A Zamfara
- Kaso 93.8% Na Masu Bayyana Ra’ayi Sun Yaba Da Sakamakon Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya
Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara da ke Abuja, karkashin jagorancin mai shari’a C.E. Nwosu-Iheme, ya kori Abbo na jam’iyyar APC.
Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta bai wa Amos Yohanna na Jam’iyyar PDP takardar shaidar cin zabe a matsayin zababben Sanata mai wakiltar yankin a Majalisar Dokoki ta kasa.
Da yake tsokaci kan tsige shi da aka yi a ranar Litinin, Sanatan ya ce ‘yan majalisa kusan biyar ne ake kokarin tsigewa saboda goyon bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari a zaben shugaban majalisar dattawa wanda daga baya Akpabio ya yi nasara.
Sai dai mai magana da yawun Akpabio, Eyiboh, a wata sanarwa a ranar Talata “ya yi watsi da ikirarin da Sanata Elisha Abbo ya yi cewa shugaban majalisar dattawa ne ya yi tasiri ga hukuncin kotun daukaka kara da ta kore shi daga majalisar.
“Sanata Akpabio ya jaddada cewa ba shi da wani mugun nufi ga wasu takwarorinsa,” in ji shi.