ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dage Takunkumin Canjin Dala Ga Masu Shigo Da Kaya 43 A Sikeli

•Yadda Abin Zai Saukaka Tsadar Rayuwa •Illarsa Ga Tattalin Arzikin Kasa

by Khalid Idris Doya
2 years ago
dala

A makon nan ne gwamnatin tarayya ta cimma matsayar janye takunkumin bayar da canjin Dala a farashin gwamnati ga ‘yan kasuwa masu shigo da kayayyakin guda 43, daga kasashen waje da suka da shinkafa, tumatir, siminti da sauran kayan masarufi.

Bisa wannan matakin, masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda suke nuni da cewa dage takunkumin na da alfanunsa da kuma akasin hakan domin kuwa a cewarsu duk da za a samu raguwar hauhawar farashi, amma manoman Nijeriya za su kara shiga cikin wani yanayi.

  • Zan Yi Fatali Da Tsare-tsaren Emefiele – Sabon Gwamnan CBN
  • Majalisar Dattawa Za Ta Tantance Sabon Gwamnan CBN Da Mataimakansa A Gobe Talata

Ana kallon wannan matakin a matsayin wani babban yunkuri da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na farfado da darajar Naira da kuma saukaka wa mutane hauhawar farashin kayan amfanin yau da kullum.

ADVERTISEMENT

Idan za a tuna dai a shekarar 2015 ne CBN karkashin tsohon gwamnanta, Godwin Emefiele ya sanya haramcin bayar da canjin Dala ga ‘yan kasuwar bisa hujjar cewa Nijeriya tana iya samar wa kanta da kayayyakin ba sain an sha wuya an nemi Dala an shigo da su ba.

Wasu masana sun yi ta sukan lamarin bisa yadda ya kara takura wa jama’ar kasa saboda rashin wadatar su a cikin kasa.

LABARAI MASU NASABA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Da yake zantawa da LEADERSHIP Hausa, Babban Masanin Tattalin Arziki, Farfesa Ahmad Sanda, da ke aiki a Jami’ar Usmanu Danfodio Sokoto, a tsangayar nazarin tattalin arziki, ya ce, janye takunkumin bayar da canjin zai sa a samu saukar farashin kayayyakin amma tabbas zai kawo babban cikas ga manoman cikin gida.
Ya ce: “Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya kai lahaula-walakuwata… domin kididdiga na baya-bayan nan da aka yi ta nuna an samu hauhawar farashin da kashi 26.4 cikin 100, ya fi shekara ashirin ba a samu irin wannan ba.

“To, ka ga shi hauhawar farashin kaya yana damun komawa musamman ma ya fi cizon talaka wanda ke da karamin karfi.

“To, ita hukuma tana ganin cewa wadannan kayan masarufi na abinci musamman shinkafa da ire-irensu idan an bude iyakoki suka shigo za a dan samu sauki, sannan ba da dama a shigo da su zai bada dama farashin kayan abinci su sauko, to ka ga ta wannan bangaren za a iya kallon matakin a matsayin abu ne mai amfani.”

“To amma ba a nan gizo ke saka ba. Ka san daya daga cikin dalilan da ya sa kayan abinci a Nijeriya ke da tsada saboda tsadar taki, tsadar kayan feshi, duk yawancin kayan da ake bukata domin yin noma sun hau. Saboda haka sai ya zama farashin abinci da ake nomawa a gida ya hau sosai.”

“Dage takunkumi da ba da dama a shigo da wadannan kayayyakin zai sa noman wadannan kayayyakin su ragu sosai, saboda ka ga wadanda za a shigo da su za su fi sauki saboda haka manoman cikin gida za su fuskanci wani kalubale ba za su iya karawa ko gogayya da kayayakin da za a shigo da su daga waje ba.

“Mafi yawan kasashen da suka ci gaba abin da suke yi domin samar da sauki a irin wannan yanayin da muke ciki shi ne su na bai wa manomansu tallafi. Saboda idan aka ce noma ya durkushe kai tsaye wadanda ake dauka aiki ba za su samu abin yi ba, rashin aikin yi musamman ga matasa zai kara kamari, kuma mun san rashin aikin yi na da illoli don bai rasa nasaba da matsalolin tsaro da muke fuskanta.

“Eh muna da bukatar mu noma kayayyakin da muke ci saboda haka ya kamata gwamnati ta bayar da tallafi musamman taki, kayan feshi, da sauran kayan noma ya zama ana bayar da su a farashi mai rahusa,” a cewar Farfesa Sanda.

Sai dai Farfesan ya ce, duk da a wasu lokutan gwamnatoci na kokarin samar da tallafin amma ana samun matsalolin rashawa, rashin adalci, da son zuciya inda suke shiga su dagula rabon ta yadda manoman ba za su amfana balle kasar ta ci gajiyar hakan.

“Matsalar da ke akwai wajen rabon takin ko da an samu tallafin shi ne wasu su kan shigo da son rai ko a ce a yi a kan siyasa ko a kan wani son rai, to ka ga hakkin gwamnati ne ta tabbatar da ta samu hanyoyin da za a raba wadannan kayan tallafin yadda abun zai kai ga talaka da yake bukatarsu domin ya yi noma ba dan kasuwa da ke bukata domin ya kai kasuwa ya sayar ba.” In ji shi.

Shi ma wani masani a bangaren tattalin arziki, Dakta Mahmud Ashiru, ya ce, “Tun da can ma mun yi ta fadan cewa ka da a rufe iyakoki, yanzu in da zan tambaya wasu alfanu Nijeriya ta samu sakamakon rufe iyakokin da aka yi a shekarun baya? Ana maganar zahiri ne, lallai an samu kuncin rayuwa sosai a kasar nan.

“Yanzu fatan da za mu yi shi ne wannan dage takunkumin ya kawo sauki ga al’ummar kasar nan domin tabbas ana cikin matsatsi sosai,” ya shaida.

Sai dai kuma, Kungiyar Masu Sarrafa Shinkafa ta Nijeriya, (RIMAN) ta nuna bacin ranta dangane da daukan matakin ba da canjin Dalar ga masu shigar da wasu kayayyaki daga kasashen waje ciki har da shinkafa.
Kungiyar masu sarrafa shinkafar ta cikin gida, ta ce matakin babbar barazana ce bayan sun zuba makudan kudi a kasuwancin.

Shugaban kungiyar, Peter Dama, ya ce, “A gaskiya wannan mataki ya zame mana kamar bala’i ne domin gwamnati ta sanya mun sanya kudadenmu mun sayi kayan sarrafa shinkafa, sannan an sa jama’a sun shiga noma shinkafar, ga shi jama’ar kasa sun fara son shinkafar da ake samarwa a gida, sai kawai mu ji an ce an dage haramcin shigo da shinkafar waje.

“Wannan mataki na gwamnati ya kawo mana cikas, ga shi kuma zai sa a rufe kamfanoni da dama, sannan jama’a da yawa za su rasa aikin yi ga shi kuma manoma da dama kuma ba za su yi aikin shinkafa, kuma sannan za a fara shigo mana da shinkafar da ta riga ta rube.”

“Gwamnati ba ta shawarce mu ba kafin ta dauki wannan mataki, kuma batun cewa shinkafar da ake samarwa a gida ma tana tsada ai kowa ya san ba da ruwa ake nomata ba, kuma yadda ake noman nata ma ai sai a duba a gani, sannan wajen ban ruwa ba wasu da kananan inji suke yi kuma ai da man fetur ake amfani a injin, kuma kowa ya san tsadar mai a yanzu.”

Shugaban ya ce babbar damuwarsu idan har aka fara shigar da shinkafar waje to mutane sai su koma kanta domin su al’ummar Nijeriya idan aka ce musu ga wani abu na waje ko da ruwan sha ne sai hankalinsu ya koma kansa.

Ya ce, “Mu mun yi iya bakin kokarin mu wajen nunawa ‘yan Nijeriya cewa shinkafarmu ta gida ta fi auki sannan ta fi amfani a jiki domin mu ta mu ba a ajiye ta ta yi shekara da shekaru ba. Mu ba ma yi wa shinkafarmu ta gida doguwar ajiya.”

“A yanzu mu matakin da za mu dauka shi ne za mu yi magana da gwamnati mu ba ta shawara, sannan mu saurara mu ji ko za su saurari kokenmu.”

“Idan har ana so a samu saukin tsadar shinkafa a kasa to sai a rage kudin man fetur da na kayan aikin gona, da kuma ba wa manoma taimakon da zai bunkasa nomansu.” In ji shi

A nashi bangaren CBN, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Abdulmumin ya fitar ya ce “Zai sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na tabbatar da daidaituwar farashi, tare da bunkasa yawan Dalar Amurka a kasuwar canjin kudaden waje ta Nijeriya ta hanyar kai dauki lokaci-lokaci”.

Tsawon shekaru masana tattalin arziki da masu zuba jari sun yi ta yekuwa don ganin an dage haramcin bayar da canjin Dalar Amurka ga masu shigar da wadannan kaya, abin da suka ce ya haifar da bambancin farashi tsakanin kasuwar ‘yan canji na bayan fage da na gwamnati.

Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, ana canjin Dalar Amurka a kan Naira1,030 a kasuwar canji na bayan fage.
Shi ma Dakta Muhammad Shamsuddeen na Jami’ar Bayero Kano ya ce labari ne mafi dadi cewa, CBN ya ce zai rika samar da Dala a kasuwa musanyar kudi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi
Hotuna

HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi

December 20, 2025
Next Post
hajjin 2024

Hajjin 2024: Wa’adin Adashin Gata Na Naira Miliyan 4.5 Ya Jefa Maniyyata Dimuwa

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.