Al’amarin da ya sa kasar Birtaniya Ingila ta hana cinikin bayi ba wani abinda zai sa a shiga mamaki ba ne domin kuwa ita bata damu da sha’anin bayi ba ita ce kasa ta farko da ta fara samun bunkasa ta bangaren masana’antu.Ba kuma wani shigo- shigo ba zurfi bane domin cigaban masana’antu ya fara ne bayan da aka hana shi cinikin bayin.
Duk da yake da Ingila ta sake dawowa inda ta mulke mu abubuwan da mulkin mallakar ya taho da su daga karshe bai yi mana dadi ba, sai suka sake dawowa kuma da kungiyoyi masu zaman kan su da Kamfanoni,
Abin dubawa anan shi n e yadda cinikin bayin ya shafe mu ba ta hanyoyi daban- daban.
- Yadda Aka Fara Cinikin Bayi (2)
- Kasashen Yamma Suna Tsotse Jinin ‘Yan Afirka Yayin Da Kasar Sin Ke Kawo Bege
Babbar matsalar da harkar cinikin bayi mana bata wuce yadda muka yi asarar mutanen da suke da basira da hangen nesa,wani abu kuma da shi na daban ne,saboda kuwa bai tabbata ba ko wadanda suka kama su sun fi su karfi ne,saboda kuwa ai sun raba mu ne da mutanen da za su iya amfani da kwakwalwarsu wajen samar da abubuwan da za su kawo ci gaban al’umma.Akwai wani babban abu da cinikin bayi ya kasa koya mana shi ne amana, da akwai rashin amana yau wanda ya zama tarihi.
Wannan rashin hadin kai wani abu ne da ya nuna gaskiyar yadda abin ya ke lokacin da Turawan yammacin Turai suka yanke shawarar su yi mana mulkin mallaka ba wani abinda ‘yan Afirka suka yi na hada kai wajen nuna adawa da shirin ba.Mutumin Nri ba zai sayar da mutumin Nri ba a matsayin bawa ba.Amma sai ga shi ya sayar da Ezza ba tare ya yi tunanin ko matakin daya dauka yana da kyau ba.
Tsohon sha’anin kasuwancin kaya da yin wasu ayyuka an yi hakan kafin a fara cinikin bayi shekaru masu yawa.Tsakanin mutumin Nri da Ezza ba wa amma kuma babu amana.
A takaice abinda cinikin bayi ya yi ma al’ummar Afirka shi ne ya hada kan ‘yan Afirka masu taimakawa Turawa,saboda sun kasa yadda za su iya zuwa da kansu wajen neman bayin,sai suka sayar da Bindigoginsu,madubansu,da giya,maganar gaskiya har da wasu kaya ga ‘yan Afirka da za su taimaka masu,wadanda za su je wurare daban- daban domin su nemo masu mutane.Irin wannan salon na neman bayi irin shi ne aka yi a yankin Neja Delta shi ne kuma mafi muni.
Yana daga cikin dalilan da suka sa har yanzu ba a amince da Igbo ba saboda salon wani hadin kai ne na al’ummar Ibo na siyasa da tattalin arziki da ya yi karfi a karni na 17 yai matukar tasiri a sashen Kudu maso gabashin Nijeriya har zuwa kusan karshen karni na 19.