Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yi gargadi kan bijirewa umarninta da Mista Marwan Ahmed, Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka a Jihar Kano ya yi.
A baya dai kotun ta bayar da umarnin a ranar 29 ga watan Satumba, inda ta haramtabwa gwamnatin jihar Kano rusa kadarorin da ke filin Idi na Kano, Kofar Mata a cikin birnin Kano.
- Da Kyar Nake Samun Yin Sallah Sakamakon Yawan Mutane Masu Korafi – El-Mustapha
- Ban Taba Tunanin Fitowa A Cikin Fina-Finan Hausa Ba -Kamaye
Lauyan da ke wakiltar Incorporated Trustees na Kungiyar Masu Mallaka da Kasuwancin Massallacin Idi, Dokta Nuraddeen Ayagi, ya garzaya kotu inda ya bukaci a yi wa Kwamishinan gargadi game da illar kin bin umarnin kotu.
Kotun ta shaida wa cewa Kwamishinan ba shi da hurumin shiga tare da lalata dukiyar da aka ambata, duk da hukuncin kotun.
Dokta Ayagi ya ce yin watsi da umarnin kotu yana zubar da mutunci da hurumin shari’a, kuma ba za ta lamunci hakan ba.
Ya ci gaba da cewa kotun na sa ran bin umarninta, kuma duk wani rashin biyayya zai haifar da sakamakon da ya dace a shari’ance.
Kotun ta tunatar da Mista Marwan Ahmed cewa rashin bin umarnin kotun na iya kai wa ga hukuncin raini.
Idan dai ba a manta ba a baya ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano karkashin mai shari’a Simon Amobeda ta yanke hukuncin cewa gwamnatin jihar Kano da KNUPDA da kuma babban lauyan jihar su hada kai su biya naira biliyan 30 ga wadanda aka rusa wa shaguna a filin Idi.
Kokarin samun martani daga babban mai shari’a na jihar Kano kuma kwamishinan shari’a Barista Haruna Isa Dederi game da lamarin ya ci tura.