Wasu alkaluma daga ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, sun nuna yadda hada hadar dakon hajoji ta tashoshin ruwan kasar ke bunkasa bisa daidaito cikin rubu’i 3 na farkon shekarar nan.
Alkaluman sun nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Satumban bana, adadin hajojin da aka yi safararsu ta tashoshin jiragen ruwan kasar ya kai tan biliyan 12.54, adadin da ya karu da kaso 8.5 bisa dari a shekara, cikin adadin, hajojin kasashen waje sun kai tan biliyan 3.77, wanda hakan ya nuna karuwar adadinsu da kaso 10.1 a duk shekara.
- Kamata Ya Yi Gwamnatin Amurka Ta Yi La’Akari Da Dalilan Karbuwar Gwamnan Jihar California A Kasar Sin
- Kasar Sin Ta Dogara Ne Kan Gaskiya Da Adalci, Za Ta Kuma Ba Da Karin Taimakon Jin Kai Zuwa Gaza
Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar sufuri ta kasar Sin Sun Wenjian, ya ce bukatuwar kasar Sin da hajoji masu yawa, na daga cikin dalilan bunkasar fannin dakon hajoji ta ruwa a kasar. Kaza lika Sun ya bayyana kyakkyawan fatan ci gaba da bunkasar hada hadar dakon hajoji ta tashoshin ruwan kasar cikin rubu’i na 4 na shekarar nan.
Jami’in ya kuma yi hasashen kara bunkasar fannin na sufurin hajoji ta tashoshin ruwan kasar ta Sin. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)