Wani Sufeton ‘yansanda, Oyebisi Bolaji, ya shaida wa wata Kotu laifin da wani mutum ya aikata na cin zarafi da cin amana a Ikeja da ke Legas. Mutumin mai shekaru 40 a duniya, Monday Daniel, ana zarginsa ne da laifin yin lalata da jikar makocinsa ‘yar shekara 13.
Bolaji, mai gabatar da kara, wacce Olufunke Adegoke ta jagoranta, ya shaida wa kotun cewa yarinyar da ke zaune tare da kakarta, wanda ake karar ya yi lalata da ita a yankin Elere Agege da ke jihar.
- CMG Ta Gabatar Da bukukuwan Baje Kolin Al’adun Sin Na Musamman A “Palace of Nations” Da Kasar Masar
- FALLASA: HUJJOJI KAN YADDA BELLO MATAWALLE YA KWASHE BILIYOYI DA SUNAN AIKIN TASHAR JIRGIN SAMA A ZAMFARA
Shaidar, har ila yau ya kuma shaida wa Mai Shari’a Abiola Soladoye cewa wani makwabcinsa, Uche Ube, ya kama wanda ake kara a lokacin da yake aikata wannan aika-aika kuma ya daga murya.
“Shi (wanda ake tuhumar) ya tashi da tsakar dare ya shiga gidan kakar yarinyar, a wannan lokaci kuma wannan makwabci nasa, Uche Ube, ya tashi ya je ya yi fitsari a lokacin da ya kama shi a saman yarinyar kafin ya yi ihu,” in ji ta.
A lokacin da ake tuhumar, mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 11 ga Oktoba, 2021.
A cewarta, laifin ya ci karo da sashe na 137 na dokar laifuka ta Jihar Legas, na shekarar 2015.
Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.