ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matasan Arewa maso Gabas Sun Ƙalubalanci Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Ayyukan Gwamnan Kano

by Sulaiman
3 years ago
Gwamna yusuf

Matasa a ƙarƙashin Ƙungiyar ‘North East Youth Progressive Union’ and Coalition for Democratic Rights Group’, sun ƙalubalanci Gwamnonin Arewa su yi koyi da irin ayyukan inganta rayuwar al’umma, wanda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa.

Matasan sun yi wannan kira a ranar Laraba, a Yola, babban birnin Jihar Adanawa, inda suka yi taron manema labarai.

  • Kwankwaso Ya Kaddamar Da Cibiyar Nazarin Harkokin Alkur’ani
  • Tsarin Canji Na Bai-daya Hanya Ce Ta Tsaftace Kasuwar Shinku

Idan za a tuna, Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin Gwamna Yusuf ta sake farfaɗo da inganta ilmin ‘ya’yan talakawa, wanda tsohon Gwamna Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ƙirƙiro a zamanin mulkin sa.

ADVERTISEMENT

Shiri ne wanda ke bai wa ‘ya’yan talakawa damammakin samun guraben tafiya karatu kyauta a jami’o’in ƙasar nan da na ƙasashen waje.

Kwanan nan Gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin ɗalibai 1001 waɗanda suka tafi ƙaro karatu a Indiya da Uganda kyauta.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Da ya ke jawabi wurin taron, Shugaban Ƙungiyar Dakta Kabir Hassan Sambo, ya nuna damuwar sa dangane da bambancin ratar samun damar ilmi tsakanin Arewa da Kudancin ƙasar nan.

Daga nan, Sambo sai ya bayar da shawarar cewa gwamnonin Arewa su gaggauta ɗaukar salo da tsarin da Gwamnatin Kano ke kai na inganta fannin ilmi, a wannan yanayi da ake fuskantar ƙalubalen rayuwar zamantakewa da ta tattalin arziki.

Sambo ya ce: “Abin dubawa ne sosai ganin yadda Gwamna Yusuf na Jihar Kano a cikin watanni biyar ya biya kuɗaɗen ɗalibai, kuɗin abincin ‘yan makaranta, kuɗin hayar ɗakunan kwanan dalibai 1001 da aka ɗauka suka tafi karatu Indiya.

“Kuma ya biya kuɗin jarabawar NECO ga ɗaliban sakandare 57,000. Sai kuma kuɗin makaranta ga ɗalibai 7,000 a Jami’ar Bayero da wasu manyan makarantu a Kano, waɗanda aka rage wa kashi 50% bisa 100% na kuɗin makarantun jami’o’i.

“Sannan kuma ya samar da cibiyoyin koyon sana’o’i ga matasa har guda 26 a faɗin jihar, domin tallafa masu a Jihar Kano.

“Gaskiya mu na buƙatar dukkan gwamnonin Arewa su yi koyi da tsare-tsaren da Kano ta ke kan yi, wajen bayar da fifiko kan ilmi da bunƙasa rayuwar al’umma.”

Kano
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

MASU ALAKA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Kano
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Kano
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Next Post
An Kama Dalibin Jami’a Da Ake Zargi Da Kashe Wani Yaro

An Kama Dalibin Jami’a Da Ake Zargi Da Kashe Wani Yaro

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Kano

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Kano

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.