A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar masanin kimiyya da fasaha na kasar Cuba, Pedro An-tonio Valdes Sosa.
A cikin wasikar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Pedro Sosa ya yi kokarin sa kaimi ga hadin gwiwar Sin da kasashen waje a fannin nazarin kimiyya da fasaha tare da samun nasarori da dama. Xi ya taya Pedro Sosa da tawagarsa murna.
Xi Jinping ya jaddada cewa, hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin kasa da kasa yana da muhimmanci a halin yanzu. Ya ce a bana ake cika shekaru 10 da Sin ta gabatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya. Kuma a cikin shekarun 10, Sin da kasashe masu raya shawarar sun gaggauta yin mu’amala a fannin kimiyya da fasaha da more ilmi, da kyautata yanayin yin kirkire-kirkire, da tarin albarkatun yin kirkire-kirkire, da sa kaimi ga hadin gwiwa a wannan fanni, da kuma samun nasarori da dama.
A kwanakin baya ne, mashahurin masanin kimiyya da fasaha na kasar Cuba, Pedro Sosa ya aika wasika ga shugaba Xi Jinping, inda ya yi bayani game da nasarorin da tawagarsa ta samu a fannonin kara azama kan nazarin ilmin kwakwalwa a kasar Sin da kuma yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Cuba ta fuskar fasahar da ke shafar kwakwalwa, yana mai bayyana cewa, yana son ci gaba da samar da gudummawa wajen sa kaimi ga sada zumunta tsakanin Sin da Cuba, da kuma aiwatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya a fadin duniya. (Zainab)