A ranar Litinin ne Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta jihar Zamfara.
A wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya karbi bayani daga kwamitin da aka kafa domin tabbatar da matsayin kudaden fansho na jihar Zamfara da na kananan hukumomi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce taron da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati da ke Gusau, an tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban jihar Zamfara.
Ya kara da cewa majalisar ta samu rahoton ci gaban da aka samu na shirin ingantawa da zamanantar da filin wasa na tunawa da Sardauna Gusau da dai sauransu.
Ya ce: “A ranar 9 ga Oktoba, 2023, Majalisar zartaswa ta Jihar Zamfara ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikata, domin tantance matsayin da Jihar Zamfara ta ke da shi na bayar da gudunmawar fansho na kananan hukumomi.
“Yayin da yake yi wa majalisar bayani, Shugaban kwamitin kuma shugaban ma’aikata na jihar Zamfara Ahmad Aliyu Liman ya bayyana cewa manufar kwamitin ita ce ta binciki zargin karkatar da kudaden da aka zaftare daga albashin ma’aikatan jiha da na kananan hukumomin jihar kan shirinsu na fansho.
“Wadannan kudade ya kamata a mika su ga masu kula da asusun fansho (PFAs) wadanda ke da alhakin kula da asusun ajiyar ma’aikata (RSAs) a jihar.
“Shugaban kwamatin ya bayyana cewa rashin fitar da kudaden ya saba wa dokar fansho ta (2014) da ke tafiyar da tsarin tafiyar da kudaden fansho kamar yadda hukumar fansho ta kasa (PenCom) ta tsara.
“Ya kuma kara nanata cewa rashin kudin da aka samu ya haifar da gazawar Hukumar Kula da Kudaden Fansho (PFAs) ta kasa biyan kudin fansho da na wadanda suka mutu yadda ya dace, wanda hakan ya haifar da koma baya ga kudaden da ba a biya ba a halin yanzu ya yi wa Gwamnatin Jiha yawa.
“Gwamna Lawal a matsayinsa na Shugaban Majalisar Zartaswa, ya bayyana aniyar bayar da tallafin da ya dace don kai dauki ga duk wani abu da ba a biya ba,” in ji shi.