Lokacin huturu, lokacin ne da jiki da fatar mutane ke wahala matuka saboda kura da iskar da ake yawan fama da ita.
Kamar yadda aka sani hunturu kan fara ne a tsakanin watan Nuwamba zuwa Maris. A irin wannan lokaci fatar mutane kan rika yakunewa yana karkarcewa wasu ma har yankewa yake wato abin da ake kira da fasau a kafar mutane.
- Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al’umma
- Hukumar Alhazai Ta Jihar Kebbi Ta Samu Sabon Shugaba
Matsalolin da irin wannan canjin yanayin ke kawowa sun hada da bashewar leben baki, tsagewar kafafen hanci, mura da dai sauran su matsaloli da ke yi wa lafiyar jiki illa.
Masana harkar lafiya sun bayyana irin matakan da ya kamata mutane su bi domin rigakafi yayin shigowar hunturu, inda suka ba da shawarar a rika saka kaya masu nauyi kuma wadanda ke rufe jiki kaf da takalma da za su rufe kafafuwa domin kare mutum daga iska.
Sun ci gaba da cewa akwai bukatar mutane su rinka shafa man kade, domin shi man kade na da ingancin hana bushewar jiki.
Wakilinmu ya zanta da babban likitan asibitin Na Kowa da ke Marabar Jos a cikin karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, Dakta Sufyan Umar Yari ya bayyana cewa, “Abin da ya kamata a duba shi ne, wadanne irin cututtuka ne aka fi samu lokaci sanyi kan manyan mutane da kuma kananan yara. Idan muka lura yanayin yana canzawa, ya kan zo da kura da iska kuma yana iya zuwa da tsananin sanyi.
“Mafi akasari dai an fi samun cututtuka da suka fi alaka da huhu irin su cutar nimoniya da asma wacce ba cuta ba ce da ake dauka a tsakanin mutane, amma dai ta fi ta shi a lokacin sanyi, saboda abin da ke ta da ta shi ne iska ko kura ko kuma shan wani abu mai sanyi,” in ji shi.
Dakta Sufyan ya ci gaba da cewa cutar nimoniya ga kananan yara ta fi tashi lokacin hunturu. Likitan ya bukaci iyaye da su takaita zirga-zirgan ‘ya’yansu da safe da kuma kula da irin kayan da ake saka musu, idan ya zama dole su fita, sai a rika saka musu kayan sanyi.
Haka zalika, ya ce, “Akwai babban kuskure da mutane suke yi lokacin hunturu na kai wuta daki ko kuma rufe daki a hana iska shigawa. Irin wannan yana haifar da matsala, saboda maimakon a kare jiki da sanyi sai kuma wata cuta da shiga. Babu wata ka’ida da ta nuna cewa dole sai mutum ya rufe ko ina kafin ya kwanta barci. Yana iya haifar da matsala musamma idan aka rufe ko ina kuma an kai wuta dakin domin shan dumin daki, to wannan abu yana haifar da matsaloli sosai.”
“Akwai magana ta wanka da ake yi wa yara a wannan lokacin hunturu, ya zama dole a rika neman dumaman ruwa ba ruwa tafasashshe ba, maimakon a yi wa yaro wanka sai a kona shi, wanda muna cin karo da irin wadannan matsaloli. Sai ka ga an kawo musu asibiti a galabaice wanda sai da kyara ake ceto rayuwarsu. An fi samun cututtuka irinsu nimoniya da bushewar makoshi da asma a lokacin hunturu, ” in ji shi.
Ya ce idan lokacin hunturu ya zo, suna bai wa mutane shawarar da rinka yawaita shan ruwa. A cewarsa, fatar Dan’adam tana aiki da ruwa, rashin yawaita shan ruwa yana haifar da tamukewar fata da bushewar makoshi.
Wasu magidanta a Jihar Kaduna sun bayyana irin hanyoyin da ya kamata a bi domin kare jiki da kamuwa daga wasu cututtukan lokacin hunturu.
Muhammadu Abdullahi magidanci ne da ke zaune a unguwar Dosa a Kaduna, ya ce lokacin hunturu akwai bukatar mutane su rika yin wanka da ruwan dumi musamman da safe ko kuma da yamma.
Ya ce za a iya cin abincin da ke dauke da kitse, fiya, kifi domin suna dauke da sinadarin da ke gyara fatar mutum.
“Kamar ni ina tabbatar da cewa kamin yarana su tafi makaranta, sai an saka musu kayan sanyi da kuma ba su abinci mai dumi. Haka ni kaina da matata duk irin matakan da muke dauka kenan lokacin hunturu. Ka ga dai yau mun tashi babu rana sai iska da hazo, wanda ya zama dole a gare ni na samar wa kaina mafita wato zan sa yi gilashi na ido da talakli mai rufi da dai sauran,” in ji shi.
Wata matar aure, Fatima Ibrahim ta ce rashin ko-in-kula da wasu iyaye mata suke yi a kan yaransu yana haifar da lalurori da yawa kama daga kamuwa da mura da masassara wadanda cututtuka ne da suke hana yara sukuni.
Ta ce a matsayinta ta uwa tana daukar matakan sanya kayan sanyi ga yaranta yayin zuwa makaranta da kuma kiyaye irin abincin da suke ci.
Fatima ta shawarci gwamnatoci da su samar da magunguna, musamma ga yara a asibitoti wanda a lokaci hunturu yara kan iya shiga halin kunci fiye da manya.
Sai dai a wani bincike da wakilinmu ya gudanar a ma’aikatar kiwon lafiya ta Jihar Kaduna, ya gano cewa lokacin hunturu ko sanyi kwakwalwar Dan’adam za ta dunga sa tsokar jiki ta rinka motsawa da sauri-sauri, wanda ake kira rawar sanyi. Amfanin hakan shi ne, samar da zafi wanda zai dumama jiki saboda haka a duk sanda wata gaba ke aiki a jikin mutum, to zafi na samuwa ta ciki kamar yadda idan ka kunna na’urar za a samu zafi.
Binciken ya nuna cewa, wannan yawan motsawar tsoka a cikin sauri lokacin da mutum ke rawar sanyi ita ce hanyar da jiki ke samar wa kansa dumi, sannan kuma a kokarin jiki na kare shigar cututtuka ta hanyar iskar da muke shaka, ya sa majina ke fita daga hancinmu.
An gano cewa a cikin iska akwai datti da kura da cututtuka iri-iri, zarar mun shaki irin wannan iskar, kwayoyin halitta da ke bututun iska da makogwaro za su gane cewa ka shaki gurbatacciyar iska, nan da nan bututun iska wanda ya fara daga kofofin hanci zuwa cikin huhu, sai ya fara samar da majina.