Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), ta ayyana ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin yajin aikin gama gari a fadin kasar nan biyo bayan cin zarafin shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero a jihar Imo.
Mataimakin shugaban NLC, Kwamared Adewale Adeyanju, da mataimakin shugaban kungiyar ma’aikata ta Nijeriya (TUC) a wani taron hadin gwiwa da ‘yan jarida a Abuja, sun bai wa gwamnatin tarayya sharuda shida domin dakile yajin aikin da za su fara.
- Xi Ya Gana Da Firaministan Girka Da Yin Tattaunawa Da Shugaban Gwamnatin Jamus
- Yadda Matata Ta Rasu A Kokarin Kare Mutuncinta Daga Masu Garkuwa – Yusuf
Daga cikin sharudan sun hada da; Korar kwamishinan ‘yansanda na jihar Imo da wasu jami’an gwamnatin jihar nan take kan cin zarafin Ajaero a jihar.
Cikakken bayani na tafe…